Rashin tsaro: Ibn Na-Allah ya nemi Gwamnati ta kai dauki a Zamfara

Rashin tsaro: Ibn Na-Allah ya nemi Gwamnati ta kai dauki a Zamfara

An farfado da wani bidiyo da aka ji Sanatan da ke wakiltar Kebbi ta kudu a majalisar dattawa, Bala Ibn Na-Allah, yana magana a game da rikicin da ake yi a jihar Zamfara mai makwabtaka da Kebbi, inda ake ta fama da kashe-kashe.

Sanata Bala Ibn Na-Allah ya koka a game da yadda gwamnatin tarayya ta tattara jami’an ‘yan sanda 30, 000 domin aikin zabe a jihar Ekiti, amma aka gaza tura manyan Dakarun jami’an tsaro da su kawo zaman lafiya a Zamfara.

‘Dan majalisar yake cewa idan har za a iya aika jami’an tsaro domin aikin zabe, ya kamata ace an jibga rundunar ‘yan sanda 10, 000 da za su yi kokarin ganin bayan Miyagun da ke Zamfara da sauran wuraren da ake kashe-kashe.

KU KARANTA: Ndume ya sake caccakar manyan Jam’iyyar APC yace akwai matsala

Rashin tsaro: Ibn Na-Allah ya nemi Gwamnati ta kai dauki a Zamfara

Sanata Bala Ibn Na-Allah tare da Buhari da wasu Sanatoci
Source: Twitter

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan yake nunawa ‘yan uwan sa a majalisar tarayyan cewa abin da yake faruwa bai dace ba. A cikin ‘yan shekarun nan dai an kashe dubunan mutane a wannan jihar inji gwamna AbdulAziz Yari.

Babban ‘dan majalisar ya kara da cewa shi da ‘yan uwan sa na APC da ke majalisar kasar, ba su ji dadin irin kashe-kashen Bayin Allah da ake yi a Zamfara. A karshen jawabin sa yace wannan abu ba ya cikin alkawarin da su kayi wa al’umma.

Ibn Na Allah yana mai tabbacin cewa shugaban kasa Buhari zai yi abin da ya dace na ganin an kawo karshen wannan rikici da ya ki ci, ya ki cinyewa. Daga baya dai gwamnatin tarayya ta tura runduna ta musamman zuwa wannan yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel