Dole Buhari yayi wa Jama’a bayanin yadda bashin Najeriya ya karu – PDP

Dole Buhari yayi wa Jama’a bayanin yadda bashin Najeriya ya karu – PDP

Mun ji labari cewa Jam’iyyar PDP mai adawa ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wa mutanen Najeriya karin bayanin yadda bashin da ake bin kasar ya karu a karkashin gwamnatin sa.

Babban Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa kudin da ake bin Najeriya ya karu daga Naira Tiriliyan 12.12 zuwa Naira Tiriliyan 24.387 daga tsakanin 2015 zuwa shekarar 2018 a mulkin APC.

Mai magana da yawun bakin na PDP yake cewa gwamnatin Buhari ta buge da cin bashi na babu gaira babu dalili a Najeriya a shekaru 3. Kola Ologbondiyan yace bashin da ke kan Najeriya ya karu da kusan Tiriliyan 12 daga 2015.

Ologbondiyan ya nuna cewa babu wani abin a zo a gani a Najeriya duk da irin tarin bashin da gwamnatin APC ta ke karbowa. A cewar sa an yi amfani da wadannan makudan kudi wajen yi wa APC kamfe a zaben da ya gabata.

KU KARANTA: Dogara yana so ayi kwaskwarimar yadda a iya tsige Shugaban kasa a Majalisa

Dole Buhari yayi wa Jama’a bayanin yadda bashin Najeriya ya karu – PDP

Buhari ya dumbuzowa Najeriya bashin Tiriliyan 13 inji PDP
Source: Depositphotos

Kakakin jam’iyyar adawar kasar ya kuma zargi gwamnatin Buhari da karkatar da sama da Tiriliyan 1.4 wajen biyan kudin tallafin fetur. Haka kuma PDP tace an yi awon gaba da sama da Biliyan 30 da aka warewa ‘yan gudu hijira.

Mista Kola Ologbondiyan yake cewa duk da irin wannan zargin badakala, ba a maganar kudi har Naira Tiriliyan 9 da ake tunani an wawura daga asusun kamfanin NNPC, don haka ya nemi majalisar tarayya ta binciki wannan lamari.

PDP ta na nan ta na sa ran cewa za tayi nasara a gaban kotu inda ta ke kalubalantar zaben 2019. Jam’iyyar adawar tana ikirarin cewa ‘dan takarar ta Alhaji Atiku Abubakar shi ne ya lashe zaben bana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel