Kashe-kashen Zamfara: Rundunar soji ta lalata sansanin yan fashi

Kashe-kashen Zamfara: Rundunar soji ta lalata sansanin yan fashi

Rundunan Sojin Najeriya, a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu tace harin da dakarunta ta kai a aikinta na Operation Diran Mikiya sun tarwatsa sansanin yan bindiga guda takwas a jihar Zamfara.

A wata sanarwa daga kakakin rundunar sojin, Air Commodore Ibikunle Daramola, a ranar 8 ga watan Afrilu 2019 ya ce an sake tura karin jiragen yaki, da niyyar fatattakar yan bindigan.

Yace rahoton masu basira ya nuna cewa sansanin yan bindigan na a jejin Sububu, Rugu, Kagara da sauransu.

Yace an tura dakarun sojin sama don tabbatar da kare rayuka da kadarorin al’umma a yankin Arewa maso yammacin kasar.

Kashe-kashen Zamfara: Rundunar soji ta lalata sansanin yan fashi

Kashe-kashen Zamfara: Rundunar soji ta lalata sansanin yan fashi
Source: Depositphotos

Daramola yace: A ranar farko da aka gudanar da aikin, ATF ta kaddamar da hari kan sansanin yan bindigan, wadanda suka hada da Doumborou, Sububu, Yammacin Malamawa, tafkin Baturia da dajin Rugu inda rundunar ta tarwatsa yawancin yan bindigan da sansanin su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10

“Jiya, ranar 9 ga watan Afrilu 2019, rundunar ta gudanar da hare-hare akan yan bindigan da dama. An kai harin farko akan wurare uku cikin jejin Subulu tare da wani sansani a jejin Kagara.

“Hari na biyu ya kai ga sansanin yan bindigan a tsaunukan Kamarawa, Kunduma da Tsamare, yayin da hari na uku ya kai ga sansanin yan bindigan dake Doumborou.

“Ya bayyana cewa rundunar ta kai taimako ga rundunar sojin kasa don basu damar shiga wurare da kama yan bindiga da kwace makaman su. A takaice, ATF ta tarwatsa sansani guda 8,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel