Kuyi hankali da yankin Igbo, Ohanaeze ta gargadi masu satar shanu

Kuyi hankali da yankin Igbo, Ohanaeze ta gargadi masu satar shanu

-Shugaba Buhari, lokacin da yake jawabi akan harin daya auku a jihar Rivers yayi kira ga jami’an tsaro da suyi aiki tukuru domin kawo karshen wannan ta’adi.

-Yan bindigan dai sun zo wajen ne akan babur har yanzu kuma ba a samu nasarar damke ko mutum daya ba.

Ministan tsaro, Mansur Dan Ali ya zargi yan siyasa da kuma masu sarautu na Arewacin kasar nan da cewa suna da hannu a cikin matsalar rashin tsaro da ake fama da ita halin yanzu, kamar yadda Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kasha kashen da akayi a jihar Rivers kuma ya bada umurnin cewa lallai hukumomin tsaro su kara kaimi don gujema aukuwar haka a nan gaba.

Haka kuma, ya sake Allah wadai ga irin wannan harin da aka kai a jihar Kaduna wanda yayi sanadiyar rasuwar mutum 20 yan yankin Adara.

Ohanaeze Ndi-Igbo

Ohanaeze Ndi-Igbo
Source: UGC

KU KARANTA:An kama malamin da yayima dalibarsa fyade

Zance daga bakin hadimin Ministan, wato Col. Tukur Gusau yace: “Duk da jajircewar jami’an tsaro da kuma wasu kungiyoyin tsaro na sa kai, wasu yan kasar nan da suka hada da ma su sarautun gargajiya da a yankunan da abin ya shafa sun kasance suna taimakawa wajen aukuwar wannan ta’addanci ta hanyar sanar da yan ta’addar wasu sirrukan da za su amfanesu wajen kai hare-hare duk domin dai su bawa jami’an soji matsala ana su yinkurin.”

Mutane ashirin da daya ne suka rasa rayukansu da kuma shanu hamsin da aka yi awon gaba dasu a harin da wasu yan bindiga suka kai a Banono da Anguwan Aku a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna ranar Litinin.

A cewar rundunar yan sandan jihar, zance daga bakin Mallam Yakubu Sabo, wasu mutum uku sun samu rauni kuma akwai gidaje goma da cinnama wuta, ya kuma kara da cewa “Yan bindigan dai sun zo wajen ne akan babur” har yanzu kuma ba a samu nasarar damke ko mutum daya ba.

Ita kuma kungiyar Ohanaeze Ndi-Igbo, PDP, Kungiyar malaman Polytechnic, Afenifere da kuma Pan Niger Delta Forum (PANDEF), sun roki Buhari da yayi amfani da mulkinsa wajen kawo karshe wannan matsal ta tsaro dake addabar kasar nan, musamman kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma ta’addanci iri daban-daban a wasu sassan kasar nan.

Shugaba Buhari, lokacin da yake jawabi akan harin daya auku a jihar Rivers yayi kira ga jami’an tsaro da suyi aiki tukuru domin kawo karshen wannan ta’adi. Ya nemi shugabannin yankunan da abin ya shafa dasu shigo ciki suma domin kwantar da tarzoma.

Akan kuwa rikicin Kaduna, a zancen da ya fito daga bakin hadimin Buhari wato Mallam Garba Shehu a Abuja yace: “Wannan kisan da ya auku tsakanin Adara da Fulani a jihar sun dade ba aminci a tsakaninsu na tsawon lokaci.”

Shugaba Buhari ya yi tir da rin wannan mummunan al’amari tsakanin dake zauna a matsayin makwabtan juna sai dai basa ga maciji wanda ke shafar yankin Kajuru da kuma Kachia.

A karshe ya baiwa yan asalin jihar Kaduna shawara da su guji daukan jita-jita da kuma zance dab a shikenan ba musamman a kafofin sadarwa na zamani wanda irin wadannan zantuka na kawo rashin zaman lafiya kuma akasarin masu yada irin wannan zance basu da sani akan abinda rikicin kan iya haifarwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel