Atiku ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kanshi

Atiku ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kanshi

- Akwai rahotanni da suke nuna cewar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya je kasar Amurka ya dakko sojojin haya, domin su zo su taya shi kwatar mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari

- To sai dai shi kuma Atikun ya fito ya karyata rahoton, inda ya ke cewa makircin jam'iyyar APC ne da ta ke so ta bata mishi suna

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya karyata jita-jitar da ake yadawa, na cewar ya aro sojojin haya daga kasar Amurka don su taya shi kwatar kujerar shugaban kasa daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya lashe zabe a watan Fabrairun da ya gabata.

A lokacin da ya ke bayyanin, wanda mai magana da yawunsa Mista Paul Ibe, ya fitar, ya ce Atiku ya bayyana cewa rahoton da aka fitar na karya ne ba shi da tushe, sannan kuma yana da tabbacin cewa jam'iyyar APC ce ta fitar jita-jitar, inda ya kara da cewa hakan ba wai sabon abu bane a wurinshi, tunda kowa ya san babu abinda jam'iyyar APC ta iya sai karya.

Atiku ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kanshi

Atiku ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kanshi
Source: Twitter

Mista Paul ya ce: "Jam'iyyar APC yanzu ta na zaune ne cikin fargaba, na tsoron kada a tona musu asiri suji kunya, shine yasa suke amfani da labaran karya domin su batawa Atiku suna, maimakon su maida hankali wurin kare kansu a kotu.

KU KARANTA: Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya

"Karar da Atiku ya kai kotu ta zame musu babbar barazana, saboda ta tona asirin jam'iyyar, akan yadda ta ke magudi, maimakon kuma su maida hankali wurin kare kansu, sai suka buge da yada labaran bogi, domin su kawar da hankulan al'umma akan irin magudin da suka yi a zaben da ya gabata.

"Babu wani labarin bogi ko jita-jita da jam'iyyar APC za ta fitar wacce za ta saka Atiku ya janye kararshi daga kotu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel