Buhari ya amince da kashe N1.3bn don biyan hakkin ma'aikatan da suka mutu

Buhari ya amince da kashe N1.3bn don biyan hakkin ma'aikatan da suka mutu

- Gwamnatin tarayya ta amince da kashe da biliyan N1.3 domin biyan hakkin ma'aikatan gwamnatin tarayya 497 da suka mutu

- Didi Walson-Jack, babban sakataren sashen walwala a ofishin shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya ne ya sanar da hakan

- A cewar Walson-Jack, gwamnati za ta fara biyan ma'aikatan kafin watan Afrilu nan da muke ciki ya kai karshe

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe biliyan N1.3 domin fara biyan hakkin ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka mutu.

Babbar sakatariyar sashen walwala a ofishin shugaban hukumar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, yayin wani taro da manyan sakatarorin ma'aikatun gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar kwadago da aka yi a Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Walson-Jack ta ce adadin wadanda za a biya din na daga cikin ma;aikata 563 da aka tantance wakilansu a ma'aikatu da hukumomi 116 tun watan Janairu.

Buhari ya amince da kashe N1.3bn don biyan hakkin ma'aikatan da suka mutu

Buhari
Source: UGC

Ta bayyana cewar za a fara biyan kudin kafin karshen watan Afilu nan da muke ciki.

DUBA WANNAN: Ziyarar Tony Blair: Mabiya Shi'a sun baibaye ofishin jakadancin Ingila

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar a yau, Laraba, ne majalisar dattijai ta amince da yin amfani da karfin ikon da take da shi domin amincewa da kudirin da ke bukatar yiwa tsarin mulki garambawul da na garambawul a bangaren kasuwancin man fetur (PIGB) bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hhannu a kansu.

Kudiran biyu na daga cikin dumbin kudirai da shugaba Buhari ya mayar wa majalisa tare da bayanin dalilinsa na kin rattaba hannu a kansu.

Majalisar na bukatar kaso biyu cikin uku (mambobi 73) na adadin jimillar sanatocin Najeriya kafin su iya yin amfani da karfin ikonsu domin tabbatar da dokokin biyu duk da shugaban kasa bai amince da su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel