Matakai 5 da gwamnati za ta dauka don samar da ingantaccen lafiya ga kowa – Kwararru

Matakai 5 da gwamnati za ta dauka don samar da ingantaccen lafiya ga kowa – Kwararru

Wasu kwararru a bangaren kiwon lafiya sun bayyana cewa inganta shirin inshoran kiwon lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na cikin dabarun da za su taimaka wa gwamnati wajen cimma manufarta na samar da kiwon lafiya mai inganci ga kowa a kasar nan.

Wadannan kwararrun sun fadi haka ne a taron tsara hanyoyin inganta kiwon lafiya da NIPPS da DRPC-PAS suka shirya a Abuja.

Jami’in gidauniyar Bill da Melinda Gates, Paul Basinga ya bayyana cewa rashin ware isassun kudade domin inganta ayyukan cibiyoyin lafiya na matakin farko, rashin ma’aikata, rashin ingantattun kayan aiki, gina asibitocin da ba za a iya kula da su ba, rashin saka mutane a cikin tsarin inshoran kiwon lafiya na daga cikin manyan matsalolin dake hana samun nasara a burin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga kowa da kowa.

Borno: Sojoji sun kwashe mazauna wani gari da ake zargin Boko Haram na buya

Borno: Sojoji sun kwashe mazauna wani gari da ake zargin Boko Haram na buya
Source: Depositphotos

Domin kauce wa wadananan matsaloli ne Basinga ya zayyano wasu matakan da za su taimaka wa gwamnati wajen cin ma burinta.

1. Ware isassun kudade domin inganta bangaren kiwon lafiya domin hakan zai kawo karshen yawan dogaro da tallafin da ake samu daga kungiyoyin ba da tallafi.

2. Tsara ingantaccen hanyar da zai taimaka wajen samar da kudaden da ya kamata domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

3. Inganta tsarin inshoran kiwon lafiya domin talakawa su amfana.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10

4. Samar da inshoran kiwon lafiyar da zai kula da kiwon lafiyar mata da yara kanana.

5. Kara mai da hankali wajen kula da adadin yawan asibitocin dake kasar nan domin ganin cewa suna aiki yadda ya kamata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel