Yan sanda sun damke wanda ake zarginsu da sace shugaban yan kwana kwana na Legas

Yan sanda sun damke wanda ake zarginsu da sace shugaban yan kwana kwana na Legas

-Musibau dai an sace shi ne ranar Assabar a Ejirin dake kan hanyar Epe-Itoikin ta Ikorodu

-Bindigogi biyu na aka samu a tare da su

Mutum biyu daga cikin wadanda suka sace shugaban yan kawana kwana na Legas, mai suna Rasaki Musibau da wasu mutum shida su ma masu garkuwa da mutane sun shiga hannun yan sanda.

An kama su ne a wani harin da rudunar ta yan sanda ta kai wanda ya hada da kwararru akan fada da masu garkuwa da mutane wanda SP Bulus R. Musa ke jagoranta a cewar mai magana da yawun yan sandan jihar Legas, Bala Elkana.

Yan sandan Najeriya

Yan sandan Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA:An rufe filin jirgin saman Legas

Musibau dai an sace shi ne ranar Assabar a Ejirin dake kan hanyar Epe-Itoikin ta Ikorodu. Su kuwa wadanda ake zargin an kama su ne ranar Laraba da misalin karfe biyar da rabi na safe.

Elkana yace: “Blessing Bayo saurayi mai shekaru 29 da kuma Smart Alfred matashi mai shekaru 32 dukkansu yan Arogbo ne ta jihar Ondo an kama su ne a kan babbar hanyar Ikorodu zuwa Ijebu Ode, garin dake kan iyaka da jihar Ogun inda dukkaninsu suka karbi laifin da ake tuhumarsu dashi.

“Bindigogi biyu na aka samu a tare da su. A halin yanzu kuma bincike na cigaba da gudana domin ganin cewa sauran yan dabar tasu da suke aikata wannan ta’asa tare su ma sun shigo hannu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel