Mulki da kudi: Saraki ya taya Aliko Dangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Mulki da kudi: Saraki ya taya Aliko Dangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa

A ranar 10 ga watan Afrelu, 1957 aka haifi shahararren dan kasuwa Aliko Dangote, tun bayan shahararsa, rahotanni suka bayyana cewa Dangote ne wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika. Wannan kuwa ya biyo bayan kasuwancin kayayyakinsa da ya ke daga Nigeria zuwa kasashen duniya.

A ranar Laraba, 10 ga watan Afrelu, Dangote ya cika shekaru 62 da haihuwa, inda shugaban majalisar dattijai na kasa Bukola Saraki ya aike masa da sakon taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

A shafinsa na Twitter, Saraki ya ce: "A yayin da kake murnar sake kara shekara daya a duniya, ina yi maka addu'ar samun daukaka, cikakkar lafiya da kuma albarka domin ci gaba da yiwa 'yan Nigeria dama duniya ayyukan jin kai."

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Shahararren marubucin Yarabawa, Oladejo Okediji ya koma ga mahalicci

Mulki da kudi: Saraki ya taya Aliko Dangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Mulki da kudi: Saraki ya taya Aliko Dangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa
Source: Twitter

Mujallar Forbes dai ta bayyana Dangote a matsayin na 100 daga cikin jerin masu kudi na duniya, kuma na daya a Afrika. Sai dai a shekarar 2014 Aliko Dangote ya gangaro har zuwa na 23 a jerin masu kudi na duniya.

A shekarar 1977 ne aka bude hadakar kamfanin Dangote, shekarar da shi kansa Dangote ya tattara ya koma Legas da zama domin bunkasa kamfanin. Kasashen da ya fi huldar kasuwanci da su sun hada da Benin, Ghana, Nigeria da Togo

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel