Kotu ta yanke ma wani dan damfarar yanar gizo hukuncin wata 1 a gidan yari kan zabar $29,000

Kotu ta yanke ma wani dan damfarar yanar gizo hukuncin wata 1 a gidan yari kan zabar $29,000

Justice Binta Mohammed ta babbar kotun Babban Birnin Tarayya, Apo a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu ta yanke hukuncin daurin wata guda ga dan damfaran yanar gizo, Obasi Wisdom, wanda aka fi sani da Jeff Peter a gidan yari kan laifin damfaran wani mai suna Douglas Guidry dala 29,000.

Justis Mohammed wacce ta yanke ma Wisdom hukunci a ranar Laraba bayan ya amsa laifinsa na damfara, ta bashi zabin biyan tarar naira 100,000.

Ya bayyana cewa bayan mai laifin ya amsa laifinsa da kuma kwace kudaden damfarar, zama a gidan yari har na tsawon wata daya ne hukuncin da ya cancance shi.

Kotu ta yanke ma wani dan damfarar yanar gizo hukuncin wata 1 a gidan yari kan zabar $29,000

Kotu ta yanke ma wani dan damfarar yanar gizo hukuncin wata 1 a gidan yari kan zabar $29,000
Source: UGC

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Wisdom a ranar 12 ga watan Afrilu, 2019 bisa laifin damfaran Mista Gudry dala 29,000.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10

Mista Mahmud Mohammed, lauyan EFCC, yace mai laifin yayi ikirarin cewa sunan shi Jeff Peters daga kasar Amurka a matsayin dan daudu kuma masoyi ga wanda ya damfara.

Lauyan yace laifin ya saba ma sashin 320(b) kuma hukunci shi na kumshe a sashi na 324 na kundin dokar kasa na 1990.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel