Da duminsa: Shahararren marubucin Yarabawa, Oladejo Okediji ya koma ga mahalicci

Da duminsa: Shahararren marubucin Yarabawa, Oladejo Okediji ya koma ga mahalicci

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu yanzu na nuni da cewa shahararren marubucin Yarabawa, Oladejo Okediji, ya amsa kiran mahalacci. Mr Okdeji ya rasu ne ba tare da wata jinya ba.

Marubucin Yarabawan, ya rasu ne a ranar Alhamis, yana da shekaru 89, kamar yadda yaronsa, Goke ya sanar da manema labarai. Goke ya bayyana cewa mahaifin nasa ya rasu ba tare da jinya ba.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni dai jama'a suka yi dandazo a gidan mamacin da ke unguwar Mabolaje da ke garin Oyo, a jihar Oyo.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Majalisar Anambra ta haramta kashe makudan kudade wajen bukin binne gawa

Marigayin Okediji, wanda ya karkatar da rubuce rubucensa akan irin tsarin littattafan baturiya, Agatha Christie, ya wallafa littattafai da suka hada da Aja Lo Leru, Rere Run, Agbalagba Akan, Atoto Arere, da Karin Kapo.

Sauran littatafan da ya wallafa sun hada da Opa Agbeleka, Oga Ni Bukola, Sango, Iroyin Ayo, Binu Tiri and a play, Aajo Aje (Zafin neman arziki), da dai sauransu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel