Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke rokon dakataccen jami’in APC a Kwara

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke rokon dakataccen jami’in APC a Kwara

- Kotun koli ta soke wani roko daga mambobin kwamitin jam’iyyar APC da aka dakatar a jihar Kwara karkashin jagorancin Ishola Balogun Fulani

- A hukuncin da aka zartar karkashin jagorancin Justis Olabode Rhodes-Vivour yace rokon bashi da inganci

- Hakan ya kasance ne saboda ba su daukaka kara cikin kwanaki 14 da doka ta tanadar ba

Kotun koli ta soke wani roko daga mambobin kwamitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka dakatar a jihar Kwara karkashin jagorancin Ishola Balogun Fulani.

Majalisar mutum biyar na kotun kolin, karkashin jagorancin Justis Olabode Rhodes-Vivour, a wani hukunci da aka yanke a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, an yi riko ga cewar rokon bashi da inganci.

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke rokon dakataccen jami’in APC a Kwara

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta soke rokon dakataccen jami’in APC a Kwara
Source: Depositphotos

Justis Olukayode Ariwoola, da yake hukunci, ya bayyana cewa rokon, kasancewarsa hukuncin wata babbar kotun tarayya da ke Ilorin, kamata yayi ace an aiwatar a cikin kwanaki 14, kamar yadda yake a karkashin oda ta 7 na dokar kotun koli.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10

Justis Ariwoola ya zartar da cewa sakamakon kin ba hukuncin kotu hadin kai, na daukaka kara cikin kwanaki 14 da aka bayar, rokon ya zama bai da fa’ida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel