Ziyarar Tony Blair: Mabiya Shi'a sun baibaye ofishin jakadancin Ingila

Ziyarar Tony Blair: Mabiya Shi'a sun baibaye ofishin jakadancin Ingila

Mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Najeriya (IMN) da aka fi kira da 'Shi'a', sun tsayar al'amura cik a kewayen ofishin jakadancin kasar Ingila da ke Abuja, a zanga-zangar nuna adawa da cigaba da tsare shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Mabiya Shi'a na zargin gwamnatin kasar Ingila da goyon bayan cigaba da tsare El-Zakzaky da gwamnatin Najeriya ke yi, sun bayyana cewar gwamnatin kasar Ingila ta cigaba da yabon shugaba Buhari, sannan bata taba cewa uffan a kan tsare shugabansu ba.

Zanga-zangar da mabiya shi'ar suka fara da misalin karfe 11:00 na safe, ta saka ofishin jakadancin rufe babbar kofar shiga ginin da suke, duk da babu wani daga ma'aikatan ofishin da ya cewa masu zanga-zangar komai.

Daga baya, mabiya shi'ar sun bar ofishin jakadancin da misalin karfe 12:00 na rana, sannan suka wuce ta gaban ofishin jakadancin kasar Amurka, China, Canada da Ghana.

Ziyarar Tony Blair: Mabiya Shi'a sun baibaye ofishin jakadancin Ingila

Mabiya Shi'a
Source: Twitter

Wani mamba a kungiyar IMN, Abdullahi Mohammed Musa, ya shaida wa manema labari cewar shirya wannan zanga-zanagar ya biyo bayan ziyarar da tsohon firaminista kasar Ingila, Tony Blair, ya kai wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Juma'ar makon jiya.

"A cikin satin da ya gabata, mun fitar da wani faifain bidiyo da Sheikh El-Zakzaky ke tona asirin kasar Amurka da Ingila da ragowar kasashe da ke da hannu a cikin kisan 'yan Najeriya, saboda kawai suna so su samu damar kwasar dukiyar Najeriya, musamman a jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 3,000 a Zamfara - Gwamna Yari

"Mun sani cewar, a ranar juma'ar da ta gabata, Tony Blair ya yi ganawar sirri da El-Rufa'i. Me suke tattauna wa? shin suna tattauna yadda za a cigaba da tsare Shekh El-Zakzaky ne don kar ya fito ya cigaba da tona masu asiri a idon 'yan Najeriya?"

"Me yake faruwa? me yasa 'yan bindigar jihar Zamfara basa sace bakin haure?", Musa ya tambaya.

Musa ya kara da cewa bakin haure sun dade suna kwasar albarkatun kasa, musamman sinadarin 'uranium' a jihar Zamfara, wanda ya ce El-Zakzaky ya dade da tona asirin faruwar hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel