Da duminsa: Majalisar Anambra ta haramta kashe makudan kudade wajen bukin binne gawa

Da duminsa: Majalisar Anambra ta haramta kashe makudan kudade wajen bukin binne gawa

- Majalisar dokokin jihar Anambra a ranar Laraba ta haramta kashe makudan kudade a wajen bukin binne gawa

- Majalisar dokokin ta ce yanzu laifi ne babba a gudanar da bukin binne gawa na sama da kwana daya

- Haka zalika, dokar ta haramta lalata kayayyaki, harbe harben bindiga, wake wake, rufe tituna da kuma hanyoyi yayin gudanar da bukin binne gawa a jihar

Majalisar dokokin jihar Anambra a ranar Laraba ta haramta kashe makudan kudade a wajen bukin binne gawa.

Da ta ke rattaba hannu kan dokar dai-daita kudaden da ake kashewa wajen binne gawa da kuma zaman makoki a jihar, majalisar dokokin ta ce yanzu laifi ne babba a gudanar da bukin binne gawa na sama da kwana daya.

Kafin wannan dokar, al'ummar jihar na gudanar da bukukuwan binne gawa har tsawon kwanaki ukku.

KARANTA WANNAN: Gani ga wane: Yadda kotu ta garkame mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama'a

Da duminsa: Majalisar Anambra ta haramta kashe makudan kudade wajen bukin binne gawa

Da duminsa: Majalisar Anambra ta haramta kashe makudan kudade wajen bukin binne gawa
Source: UGC

Sai dai wanda ya gabatar da dokar, mamba mai wakiltar mazabar Anaocha II, Charles Ezeani ya bayyana cewa "dokar za ta taimaka wajen rage kudaden da ake kashewa wajen bukin binne gawa a jihar."

Dokar ta bayyana cewa a yayin bukin binne gawa, "ba a yarda wani ya ajiye gawa a dakin ajiye matattu har sama da watanni biyu bayan mutuwar ba, yayin da bukin binne gawar zai zama na rana daya kawai."

Haka zalika, dokar ta haramta lalata kayayyaki, harbe harben bindiga, wake wake, rufe tituna da kuma hanyoyi yayin gudanar da bukin binne gawa a jihar.

Dokar ta kuma bayyana cewa, "Ba a yarda 'yan uwan mamacin su shafe sama da mako daya suna zaman makoki ba daga ranar da aka binne gawar mamacin."

Da ya ke zantawa da manema labarai, Ezeani ya ce za a kafa kwamitin da zai sa idanuwa don tabbatar da cewa dokar ta yi aiki kan kowa da zaran gwamnan jihar ya rattaba hannu akanta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel