Gani ga wane: An daure matashin da yayi ma yar shekara 9 fyade shekaru 21 a Kurkuku

Gani ga wane: An daure matashin da yayi ma yar shekara 9 fyade shekaru 21 a Kurkuku

Wata babbar kotu dake zamanta a unguwar Kasuwan Nama dake cikin garin Jos jahar Filato ta yanke ma wani matashi mai sana’ar kanikanci, Abdulrahman Mustapha hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru ashirin daya bayan ta kamashi da laifin yi ma wata yarinya fyade.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, Yahaya Mohammed ya yanke ma Mustapha wannan hukunci ne sakamakon kamashi da laifin yi ma yarinya mai shekaru 9 fyade, inda yace hakan zai zamto izina ga na baya.

KU KARANTA: Kalli wasu yan fashi da makami da aka kama sanye da kayan jami’an Yansanda

Da fari, lauya mai shigar da kara, Ibrahim Gokwat ya bayyana cewa a ranar 5 ga watan Afrilu ne wani mutumi mai suna Yusuf Dada mazaunin kauyen Rikkos ya kai ma Yansandan Laranto kara game da abinda bakaniken yake aikatawa.

Lauya Gokwat yace bakaniken ya yaudari karamar yarinyar ne da nufin zai aiketa ta sayo masa ruwa, inda ya kamata da karfi da yaji ya shigar da ita wani kango, a can yayi mata fyaden.

Haka zalika Lauya Gokwat ya bayyana ma kotu cewa ba akan yarinyar wannan bakaniken ya fara fyade ba, inda yace “An taba kama wannan mutumin da aikata fyade akan wata karamar yarinya mai shekaru 13 a lokacin da take barci.”

Don haka lauyan ya nemi kotu ta hukunta bakaniken da tsatstsauran hukunci don hakan ya zama darasi a gareshi, da ma duk masu tunanin aikata irin wannan aika aika, musamman ganin cewa laifin ya saba ma sashi na 257 na kundin hukunta manyan laifuka.

Sai dai shima wanda ake tuhuma da laifin aikata fyaden, bakanike Abdulrahman Mustapha bai baiwa shari’a wahala ba, inda ya amsa laifinsa nan take, amma ya nemi ayi masa sassauci.

Daga karshe bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu ne sai Alkalin kotun, Yahaya Muhammad ya sanar da yanke masa bakaniken hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari, tare da horo mai tsanani, kuma babu zabin tara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel