Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kashe-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10

Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kashe-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10

Majalisar dattawa a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, sannan ta yabi yan Najeriya akan fitowa da suka yi kwansu da kwarkwatansu don taya al’umman jihar yin zanga-zanga.

Yayinda Sanata Kabiru Garba Marafa (APC, Zamfara) ya gabatar da lamarin, Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zo da wani shiri na shekaru 10 don kula da yan gudun hijira a jihar.

Majalisar har ila yau ta yanke shawaran kaddamar da ayyuka na naira biliyan 10 a kasafin kudin kasa ga wadanda hare-haren yan bindiga ya shafa.

Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10

Yanzu yanzu: Majalisar dattawa tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, ta bukaci shirin sake gine-gine na shekaru 10
Source: Depositphotos

Marafa da yake bayani kan lamarin ya bayyana yanda yan bindiga ke kashe mutane a jihar Zamfara kusan kullun.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar PDP ya kalubalanci nasarar Gwamna Shettima a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya

Yace lamarin yasa mutane da yawa sun zama marasa galihi kamar yanda suka bar kauyukan su don neman mafaka a sauran wurare, inda ya bayyana cewa lamarin ya kasance abun tausayi.

Sanatoci wadanda suka yi muhawarar da sun koka kan rashin tsaro ba a Zamfara kadai ba, har da sauran jihohi kamar Kaduna, Katsina, Sokoto, Plateau, Benue, Taraba, da sauran su.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa majalisar dattijai ta amince da yin amfani da karfin ikon da take da shi domin amincewa da kudirin da ke bukatar yiwa tsarin mulki garambawul da na garambawul a bangaren kasuwancin man fetur (PIGB) bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hhannu a kansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel