Nnamdi Kanu ya yi martani a kan umurnin da kotu ta bayar na kamo shi

Nnamdi Kanu ya yi martani a kan umurnin da kotu ta bayar na kamo shi

Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra, (IPOB) ya ce umurnin da kotun Najeriya ta bayar na kamo shi ba zai yi tasiri ba ko kadan.

Ana tuhumar Kanu tare da wasu masu neman kafa Biafra ne da laifin cin amanar kasa hakan yasa ya tsere bayan an bayar da shi beli amma daga bisani ya bulo a kasar Isra'ila.

Alkaliyar kotu, Justice Binta Nyako ta yanke hukuncin janye belin da aka bashi tare da bayar da umurnin a kamo shi duk inda ya ke ne sakamakon rashin bayyanarsa a kotu domin cigaba da shari'arsa.

Nnamdi Kanu ya yi martani kan umurnin da kotu ta bayar da kamo shi

Nnamdi Kanu ya yi martani kan umurnin da kotu ta bayar da kamo shi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kotu ta janye belin Nnamdi Kanu, ta bayar da umurnin a cafko shi

Sai dai a jawabin da ya yi ta kafar Rediyo Biafra da The Cable ta jiyo, Kanu ya ce dokar kama shi ba za tayi tasiri a kasashen waje ba.

"A watan Maris na 2017, Kotun kiyaye hakkin bil adama na kasa da kasa ta umurci gwamnatin Najeriya ta dena tuhumar mambobin IPOB ciki har da ni amma har yau gwamnatin ba tayi biyaya ga wannan dokar ba," inji shi.

"Umurin da aka bayar na kama ni ba zai yi tasiri ba. Ina kyautata zaton kasashen waje da suka dade suna nuna rashin amincewa da abinda ake yiwa IPOB a Najeriya za suyi watsi da umurnin.

"Neman 'yancin kai ba laifi bane domin sashi na A9 na dokar Najeriya na 2004 ya halasta hakan. Saboda haka mai yawa Justice Binta Nyako za ta bayar da umurnin a kamo shi idan har tana da niyyar biyaya ga dokar Najeriya da ya bani damar neman kafa Biafra?."

Kanu ya yi ikirarin cewa yana da mabiya masu yawa a Najeriya kuma har yanzu suna nan kan bakarsu ta neman kafa kasar Biafra.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel