An kama malamin da yayima dalibarsa fyade

An kama malamin da yayima dalibarsa fyade

-An sanar damu cewa wanda ake zargin ya tafi ofishin yan sanda da lauya da tunanin cewa hakan zai bashi dammar samun beli.

-Oyeyemi yace:Eh, tabbas mutumin yana hannu kuma Kwamishina ya bada umurnin a mika shi zuwa ga sashen

Wani tsohon malamin makarantar Isolog Group of Schools, Agbole Akute dake jihar Ogun wanda ya tsere akan zargin da akeyi masa nayin lalata da daliban makarantar ya shiga hannun hukuma.

Wanda ake zargin mai suna, Adebayo Gbadebo, ya shiga hannun hukuma ne a daren Litinin bayan da aka matsayawa hukumar makarantar cewa lallai sai ta nemo shi, hakan kuwa akayi.

Adebayo Gbadebo

Adebayo Gbadebo
Source: UGC

KU KARANTA: Ku manta da takarar shugabancin kasa a 2023, Okorocha ga kabilar Igbo

An sanar damu cewa wanda ake zargin ya tafi ofishin yan sanda da lauya da tunanin cewa hakan zai bashi dammar samun beli.

Jaridar The Nation that fahimci cewa lauyan ya bukaci a sake yin wani gwajin a asibiti akan wanda abin ya faru da ita, wanda da farko an kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (wato LASUTH) yayin da ake zargin anyi batanci da yarinyar a wannan lokacin.

Da yake tabbatar da kama wanda ake zargin mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar, wato DSP Abimbola Oyeyemi ya shaidawa wakilinmu cewa Kwamishinan yan sanda ya bayar da umurnin cewa a mika wannan badakkala zuwa ga sashen dake kula da safarar yara da kuma kare hakkin dan adam na jihar wato (SCIID) domin gudanar da nasu binciken.

Ya tabbatar mana cewa wanda ake zargin da lauyansa yazo inda ya bukaci a sake gudanar da wani gwajin akan yarinyar da abin ya faru da ita sai dai ba a karbi korafin nasa ba saboda ofishin yan sanda ba kotu bane, haka kuma baza su bar yarinyar ta shiga wani hali ba da ka iya bata matsala har ma ya shafi lafiyarta.

Oyeyemi yace: “Eh, tabbas mutumin yana hannu kuma Kwamishina ya bada umurnin a mika shi zuwa ga sashen kula da yancin bil adama da kuna hana safarar kananan yara domin karin bincike.

“Sun zo tare da lauya kuma bamu amince da wasu daga cikin bukatunsu ba. Sun nemi sake yin gwaji ga yarinyar a wani wurin gwaji na daban, sai muka fada masu ba a kotu muke hakan ba zai samu ba, a halin yanzu badakkalar na karkashin kulawar sashen hana safarar kananan yara da kuma kare hakkin bil adama ta SCIID don gudunar da kwareren bincike.

“Makarantar ce ta kawo shi bayan matsin lamba daga wurin yan sanda na cewa lallai sai sun kawo shi. Makarantar ta rufe laifin ne lokacin da abin ya faru sai dai kawai sallamarsa da tayi shikenan."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel