Kin rattaba hannu a kan wasu dokoki 2: Majalisa za tayi amfani da karfin ikonta a kan Buhari

Kin rattaba hannu a kan wasu dokoki 2: Majalisa za tayi amfani da karfin ikonta a kan Buhari

- Majalisar dattijai ta bayyana cewar za tayi amfani da karfin ikon da ya bata damar tabbatar da doko ko babu amincewar shugaban kasa

- Hakan ya biyo bayan watsi da wasu kudiri biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi

- Mjalisar na bukatr goyon bayan mambobi 73 (kaso biyu bisa uku) kafin samun damar tabbatar da dokokin

A yau, Laraba, ne majalisar dattijai ta amince da yin amfani da karfin ikon da take da shi domin amincewa da kudirin da ke bukatar yiwa tsarin mulki garambawul da na garambawul a bangaren kasuwancin man fetur (PIGB) bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hhannu a kansu.

Kudiran biyu na daga cikin dumbin kudirai da shugaba Buhari ya mayar wa majalisa tare da bayanin dalilinsa na kin rattaba hannu a kansu.

Kin rattaba hannu a kan wasu dokoki 2: Majalisa za tayi amfani da karfin ikonta a kan Buhari

Majalisar dattijai
Source: Depositphotos

Majalisar na bukatar kaso biyu cikin uku (mambobi 73) na adadin jimillar sanatocin Najeriya kafin su iya yin amfani da karfin ikonsu domin tabbatar da dokokin biyu duk da shugaban kasa bai amince da su ba.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 3,000 a Zamfara - Gwamna Yari

Kazalika, majalisar ta yanke shawarar yin gyara a kan wasu kudiri 11 domin sake mayar da su ga shugaba Buhari domin ya amince da su.

Majalisar ta bayyana cewar zata yi watsi da kudiri hudu da shugaba Buhar ya ki saka wa hannu.

Hakan ya biyo bayan amince wa da rahoton kwamitin adalci da Sanata David Umaru (dan jam'iyyar APC daga jihar Neja) ke jagoranta da majalisar ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel