Boko Haram sun kashe dan sanda, sunyi garkuwa mutane masu yawa a Nijar

Boko Haram sun kashe dan sanda, sunyi garkuwa mutane masu yawa a Nijar

Mayakan kungiyar Boko Haram sunyi garkuwa mutane da dama tare da kashe wani jami'in dan sanda guda daya a wata hari da suka kai a yankin Kudu maso Gabashin Nijar kamar yadda wani babban jami'i ya shaidawa AFP a ranar Laraba.

'Yan ta'addan da ake kyautata zaton wasu daga cikinsu na sanye da rigar bam sun kai hari ne a sassan birnin Diffa tun daren Talata zuwa safiyar ranar Laraba inji jami'in.

Mazauna garin sun bayyana cewa sun rika jin karar fitar harsashin bindiga da fashewar bama-bamai a kusa da caji ofis din 'yan sanda.

Rahotanni sun ce an kashe biyu daga cikin 'yan ta'addan.

Boko Haram sun kashe dan sanda, sun sace mutane masu yawa a Nijar

Boko Haram sun kashe dan sanda, sun sace mutane masu yawa a Nijar
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Reshe ya juye da mujiya: Sojoji sun bi sahun 'yan Boko Haram da su kayi yunkurin kai hari a Damataru

"Maharan da jami'an tsaro suka tunkara sun nemi mafaka a gidan wani jami'in dan sanda kuma sunyi garkuwa da mutane masu yawa," a cewar jami'in gwamnatin da ya nemi a boye sunansa.

Wani mazaunin garin Diffa ya shaidawa AFP cewa 'yan suna kokarin 'cin galaba a kan 'yan ta'addan.

Diffa yana kusa da Arewa maso Gabashin Najeriya ne kuma yana da iyaka da Tafkin Chadi. Boko Haram sun dade suna kai hari a garin.

A kalla mutane 27,000 sun rasu kuma 2,000,000 sun rasa muhallinsu tun lokacin da Boko Haram suka fara kai hare-hare a Arewa maso Gabashin Najeriya a 2009. Yanzu kuma hare-haren ya yadu zuwa Nijar, Burkina Faso da Chadi.

A kasar Nijar, Boko Haram sun kashe mutane 88 a cikin watan Maris sannan fiye da mutane 18,000 sun bar kauyukansu a cewar Majalisar Dinkin Duniya, UN.

UN din ta ce tana matakur damuwa a kan tsaro ke tabarbarewa a yankin na Diffa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel