Hukumar sojin sama sun yiwa yan barandan Zamfara luguden wuta (Bidiyo)

Hukumar sojin sama sun yiwa yan barandan Zamfara luguden wuta (Bidiyo)

- Yan barandan jihar Zamfara sun kirawa kansu ruwa

- Dakarun Sojin saman NAjeriya sun kai hari mabuyarsu 8 a cikin dajin jihar

Hukumar sojin saman Najeriya ta samu nasarar kai gagarumin hari kan yan bindigan da suka addabi mutanen jihar Zamfara.

Kakakin hukumar sojin saman, Ibikunle Daramola, ya bayyana cewa ana cigaba da samun nasara a atisayen DIRAR MIKIYA da hukumar ta kaddamar domin kawar da yan barandan jihar Zamfara.

A wani jawabi da ya saki, ya bayyana yadda suka kaiwa hare-hare dajin Sububu, Rugu, Kagara, Doumborou, Malamawa da Baturia inda aka hallaka yan bindiga da dama.

Yace: "Luguden wutan da aka yi ranar 8 ga watan Afrilu, 2019 domin kawar da yan barandan a mabuyarsu dake dazukan Sububu, Rugu, da Kagara domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar yankin Arewa maso yamma."

"A ranar farko, jami'am ATF sun kai hari mabuyar yan barandan dake Doumboru, Sububu da Malamawa, tafkin Baturiada dajin Rugu, inda aka halaka yan bindigan da dama."

A ranar 9 ga watan Afrilu, 2019, jami'an ATF sun kai hari wurare daban-daban. Na farko ya hallaka yan bindiga 3 a dajin Sububu, sannan wani mazauninsu a dajin Kagara."

An kai hari na biyu mabuyarsu dake tsaunin Kunduma da Tsamare, sannan aka kai na ukun Doumborou."

Sannan jai'an ATF suka taimakawa jami'an sojin kasa wajen shiga wuraren da aka kai hari domin damke yan barandan da suka rage da kwace makamansu. A karshe, an lalata mabuyar su 8 kuma an kashe da yawa cikinsu."

Rahotanni sun nuna cewa sakamakon wadannan hare-hare, an ga wasu yan barandan suna guduwa iyakan Najeriya da kasar Nijar. Kana hukuma ta hana kai da jami'an kasar Niar wajen hanasu samun shiga ta kudancin kasar.

Kalli bidiyon:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel