Kotu ta bayar da umurnin tsare makiyaya a kurkuku saboda satar katin waya

Kotu ta bayar da umurnin tsare makiyaya a kurkuku saboda satar katin waya

A yau Laraba ne wata kotun majistare da ke Ilorin ta bayar da umurnin a tsare wani makiyayi mai shekaru 25, Mohammed Bello a gidan yari na Oke-kura bisa zarginsa da satar katin waya na N420,000.

'Yan sanda suna tuhumar Bello mazaunin Ago-Are, Igebti a jihar Oyo da laifin hadin baki da fashi da makami.

Shugaban kotun, Mrs Aminat Issa ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Kotu ta bayar da umurin tsare wani makiyayi da ya saci katin waya

Kotu ta bayar da umurin tsare wani makiyayi da ya saci katin waya
Source: Twitter

A baya, dan sanda mai shigar da kara, Sufeta James Odaudu ya shaidawa kotu cewa wani Sunday Edeh da ke gidan Jowuro a garin Banni ne ya shigar da kara a caji ofis din Banni.

Ya ce wanda ya shigar da karar ya yi ikirarin wasu makiyaya biyu sun yi masa fashi inda suka sace katin waya da kudinsu ya kai N420,000, wayan salula uku da kudinsu ya kai N33,500 sai kuma karamin rediyo da kudinsa ya kai N3,000.

Mai shigar da karar ya ce mazauna kauyen ne suka kaiwa wanda ya shigar da karar dauki inda suka kama wanda akayi kararsa amma abokin laifinsa ya tsere.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a yayin da 'yan sanda ke masa tambaya inda ya ce sunan wanda suka tafi fashin tare Susu.

Odaudu ya ce laifin ya sabawa sashi na 6(b) da 1(2) na dokar fashi da makami.

Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifinsa a kotun kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel