Zan bar jihar Kwara fiye da yanda na same ta – Gwamna Ahmed

Zan bar jihar Kwara fiye da yanda na same ta – Gwamna Ahmed

Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara, a jiya, Talata, 9 ga watan Afrilu, yace koda dai akwai kalubalen tattalin arziki a kasar wanda ya shafi gwamnatinsa na shekaru takwas, gwamnatin nasa zata bar jihar fiye Da yanda ya same ta.

Gwamna Ahmed na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda zai kammala shekarunsa na takwas a matsayin gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayu, 2019, zai mika mulki ga Alhaji Abdulahman Abdulrazak na jam’ iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya lashe zaben gwamna a zaben da ya gabata.

Gwamnan wanda yayi magana a lokacin rantsar da mambobin 24 na kwamitin mika mulki ga sabon gwamnati a jihar.

Zan bar jihar Kwara fiye da yanda na same ta – Gwamna Ahmed

Zan bar jihar Kwara fiye da yanda na same ta – Gwamna Ahmed
Source: UGC

Gwamnan, wanda yace anyi shirin ne don taimaka wa gwamnati mai zuwa wajen ganin ta samu wajen zama cikin gaggawa, ya bukaci mazauna jihar da su ba gwamnatin mai zuwa hadin kai kamar yadda suka ba gwamnatinsa, “domin jihar Kwara ta ci gaba akan tafarkin ci gaba.”

KU KARANTA KUMA: Dan takarar PDP ya kalubalanci nasarar Gwamna Shettima a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sam ba zai damu ba don an kira shi da 'Baba go slow' ma damar dai ba za a kira sa barawon dukiyar kasar ba.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Talata, a yayin da ya ke amsa tambayoyi a wajen taron da ya gudana tsakaninsa da 'yan Nigeria mazauna Dubai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel