Jami’an tsaron da ke Zamfara ba su da wani tasiri - Sarakunan Jihar

Jami’an tsaron da ke Zamfara ba su da wani tasiri - Sarakunan Jihar

Shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmad, ya bayyana cewa sojojin da ‘yan sanda da aka tura jihar ba su da wani amfani.

Sarkin ya bayyana haka ne a taron ziyarar da Babban Sufeton ’yan sanda na kasa, Muhammad Adamu, ya kai jihar a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu, don ganin kamo bakin zare kan matsalar tabarbarewar tsaro a jihar.

Sarkin Zamfara Ankan ya ja kunnen shugabannin tsaro a kan cewa, “wannan taron shi ne karo na bakwai, kuma babu wani abinda ya sauya. Saboda haka daga yanzu goron gayyatar murnar magance matsalar tsaro ce za mu amsa, amma ba ta wata daban ba."

Jami’an tsaron da ke Zamfara ba su da wani tasiri - Sarakunan Jihar

Jami’an tsaron da ke Zamfara ba su da wani tasiri - Sarakunan Jihar
Source: UGC

Sarkin ya kuma bayyana wa sufeto janar din cewa, “duk fadin jihar Zamfara ba mu da ’yan sanda dubu uku, babu karamar hukumar da ke da ’yan sanda dari da hamsin. Ta yaya za su kare Zamfarawa Miliyan hudu?”

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta yanke jiki ta fadi yayinda take fada da kishiyarta a Kano

Don haka ya nuna rashin gamusuwar su da yadda jami’an tsaro ke nuna halin ko’in-kula a kan kashe rayukan al’ummar jihar Zamfara da garkuwa da su.

A baya Legt.ng ta rahoto cewa, kungiyar masu hakar ma’adinai ta Najeriya, tace za ta ba Gwamnatin Tarayya hadin kai, kan umurnin da tayi na tsayar da ayyukan hake-hake a Zamfara nan da sa’o’i 48. Alhaji Kabir Kankara, babban shugaban kungiyar na kasa ya bayyana hakan nea ranar Talata, 10 ga watan Afrilu a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta tuna a baya cewa Gwamnatin Tarayya ta ba da umurni akan dakatar da dukkan ayyukan hake-hake a Zamfara nan da sa’o’i 48, a ranar 7 ga watan Afrilu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel