Dan takarar PDP ya kalubalanci nasarar Gwamna Shettima a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya

Dan takarar PDP ya kalubalanci nasarar Gwamna Shettima a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya

- Dan takarar PDP, Sanata Mohammed Abba-Aji, ya roki kotun zabe na jihar Borno da ta soke nasarar Gwamna Kashim Shettima na APC, a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya

- Abba-Aji yayi korafin cewa akwai zaben da ya wuce kima a yankuna bakwai sannan akwai hujja na ayyukan da suka saba ma dokar zabe

- Dan takarar na PDP ya nemi kotu ta janye takardar cin zabe da INEC ta bai wa Shettima sannan a sake sabon zaben sanata a yankin

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Mohammed Abba-Aji, ya roki kotun sauraron kararrakin zabe na jihar Borno da ta soke nasarar Gwamna Kashim Shettima na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Abba-Aji, ya taba wakiltan yankin tsakanin 2003 da 2007.

Dan takarar PDP ya kalubalanci nasarar Gwamna Shettima a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya

Dan takarar PDP ya kalubalanci nasarar Gwamna Shettima a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Borno ta tsakiya
Source: Twitter

A wani korafi mai lamba EPT/BO/SEN/3/2019 dauke da kwanan wata 17 ga Maris, wanda aka gabatar a gaban kotun zabe da ke zama a Abuja, Abba-Aji yayi korafin cewa akwai zaben da ya wuce kima a yankuna bakwai sannan akwai hujja na ayyukan da suka saba ma dokar zabe.

Cikin wadanda aka sanya a karan harda APC da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

KU KARANTA KUMA: Zamfara: Za mu ba gwamnatin tarayya hadin kai – Shugaban kungiyar masu hakar ma’adinai

Abba-Aji na neman umurnin kotu, da ta sa INEC janye takardar shaidar cin zabe da tab a Shettima saboda akwai magudi a zaben kuma bai bi ka’idar dokar zabe ba.

Ya kuma nemi wani bukata da zai sa INEC ta gudanar da sabon zabe na kujerar sanata a yankin Borno ta tsakiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel