Cikin kwanaki 60: Kotu ta umurci hukumar NIS da ta biya wani tsohon ma'aikacinta N9.7m

Cikin kwanaki 60: Kotu ta umurci hukumar NIS da ta biya wani tsohon ma'aikacinta N9.7m

- Kotu ta baiwa hukumar NIS umurnin biyan wani tsohon ma'aikacin hukumar, kudadensa na albashi da sauran hakkokinsa da suka kai N9.7m

- Albashin, kamar yadda kotun ta bayar da umurni, zai fara ne daga 1 ga watan Yulin 1999 zuwa 31 ga watan Ogusta, 2014

- Haka zalika ta bukaci hukumar da ta biya Made N2m a matsayin barnar da aka yi masa da kuma N250,00 a matsayin kudin kara

Kotun masana'antu ta kasa da ke da zama a Abuja, a ranar Larabar nan ta baiwa hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) umurnin biyan wani tsohon ma'aikacin hukumar, Oguntyoyinbo, kudadensa na albashi da sauran hakkokinsa da suka kai N9.7m. Kotun ta baiwa hkumar wa'adin kwanaki 30.

Albashin, kamar yadda kotun ta bayar da umurni, zai fara ne daga 1 ga watan Yulin 1999 zuwa 31 ga watan Ogusta, 2014.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa an dauki Made aiki a ranar 1 ga watan Nuwamba, 1993 a matsayin sifeta na hukumar shige da fice a 'Conpass 07'.

KARANTA WANNAN: Buhari: Zan iya zama 'Baba go slow' amma dai ba za a taba kirana barawo ba

Cikin kwanaki 60: Kotu ta umurci hukumar NIS da ta biya wani tsohon ma'aikacinta N9.7m

Cikin kwanaki 60: Kotu ta umurci hukumar NIS da ta biya wani tsohon ma'aikacinta N9.7m
Source: Depositphotos

Made ya shigar da kara kotun inda ya bukaceta da ta duba lamarinsa bayan da aka cire shi daga aikin gwamnati sakamakon wani shiri da aka gudanar a watan Afrelun 1999.

Duk da cewa an mayar da shi aiki a shekarar 2003, ba a mayar da shi cikin ayyukan yau da kullum na hukumar ba, kuma baya daga cikin wadanda ake karawa matsayi.

Sai dai, mai shari'ar da ya yanke hukuncin karar a watan Yunin 2014, ya umurci hukumar da ta dauki wanda ya shigar da karar a matsayin ma'aikacinta. Wannan umurnin ne ya sa aka mayar da Made aiki, amma ba a biya shi albashi ba tun daga watan Yulin 1999 har zuwa Ogusta, 2014, kamar yadda bangaren lauyoyinta ya bukata.

Amma a sabon hukuncin da kotun ta yanke, mai sharia'ar ta ce: "Wanda ya shigar da karar ya na da hujjojin da tilas kotun ta umurci hukumar ta biya shi N9.705m.

"Bisa ga hujjojin da aka gabatar, a wannan gabar, na yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da kara ya cancanci a biya sa hakkokinsa."

Haka zalika ta bukaci hukumar da ta biya Made N2m a matsayin barnar da aka yi masa da kuma N250,00 a matsayin kudin kara. A karshe ta bukaci hukumar da ta biya kudaden cikin kwanaki 60, gazawar hakan kuma zai kara yawan kudaden da kashi 21.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel