An rufe filin jirgin saman Legas

An rufe filin jirgin saman Legas

-Mai magana da yawun rudunar yan sandan filin jirgin saman, mai suna Joseph Alabi ya tabbatar da rufe titin dake sadarwa zuwa tasahar jirgin da masu zanga-zangar sukayi.

-Babban Sakataren NUATE, Kwamared Aba Ocheme, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa mambobinsu goma sha biyu ne hannun yan sanda.

Mambobin kungiyar safarar jiragen sama wato (NUATE) jiya sun rufe tashar jirgin saman Murtala Muhammad bisa ga kama wasu mambobin kungiyar

Jami’an yan sanda ne suka kame yan kungiyar tasu da su karkashin Caverton Helicopters. Mambobin wannan kungiya sunyi zanga zangar nuna rashin amincewa da kama mutanensu da akayi a sararin filin jirgin saboda rashin biyansu hakkinsu da ba ayi ba.

Filin jirgin saman Murtala na Legas

Filin Jirgin Legas
Source: UGC

KU KARANTA:Shin zababben Gwamnan Adamawa Fintiri, ya shirya kuwa?

Babban Sakataren NUATE, Kwamared Aba Ocheme, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa mambobinsu goma sha biyu ne hannun yan sanda.

Kungiyar tasu ta kasha hanyar dake isarwa zuwa ga tashar jirgin na tsawon awa daya domin nuna rashin amincewarsu kan wannan al’amari, hakan nema ya janyo cinkoso akan titin ta bangaren kofar shiga filin jirgin.

“ A shirye muke da mu tunkari Caverton da Yan sandan Najeriya akan wannan lamari,” a cewar NUATE.

Mai magana da yawun rudunar yan sandan filin jirgin saman, mai suna Joseph Alabi ya tabbatar da rufe titin dake sadarwa zuwa tasahar jirgin da masu zanga-zangar sukayi.

Kana kuma ya bayyana cewa tawagar yan sandan da ta kama mambobin kungiyarsu na karkashin rudunar yan sandan Jihar Legas ne, ya kuma kara da cewa yan sandan sun kasance a wurin ne domin jaddada tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel