Buhari: Zan iya zama 'Baba go slow' amma dai ba za a taba kirana barawo ba

Buhari: Zan iya zama 'Baba go slow' amma dai ba za a taba kirana barawo ba

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sam ba zai damu ba don an kira shi da 'Baba go slow' ma damar dai ba za a kira sa barawon dukiyar kasar ba

- Shugaban kasar ya ce yana tafiyar hawainiya ne domin ya rayu saboda gudun maimaita kuskuren da ya yi a lokacin mulkin soja da ya jefa sa a kurkuku

- Buhari ya tunatar da su yadda ya yi takarar shugabancin kasar har sau ukku bai samu nasara ba, sai a karo na hudu ne ya lashe zaben

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sam ba zai damu ba don an kira shi da 'Baba go slow' ma damar dai ba za a kira sa barawon dukiyar kasar ba. Shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Talata, a yayin da ya ke amsa tambayoyi a wajen taron da ya gudana tsakaninsa da 'yan Nigeria mazauna Dubai.

"Za a iya kirana 'Baba go slow' amma ba dai barawo ba," a cewar Buhari.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa yana tafiyar hawainiya ne domin ya rayu saboda baya son ya sake maimaita irin kuskuren da ya yi a lokacin da ya ke shugaban kasa na mulkin soja, inda har gaggawarsa ta jefa sa kurkuku.

KARANTA WANNAN: Kakakin majalisar wakilai: Dattawan Arewa ta tsakiya sun goyi bayan Idris Wase

Buhari: Zan iya zama 'Baba go slow' amma dai ba za a taba kirana barawo ba

Buhari: Zan iya zama 'Baba go slow' amma dai ba za a taba kirana barawo ba
Source: Facebook

"Don haka, duk wanda ya kirani 'Baba go slow', to ya sani ina taka tsantsan da tsoron kar tarihi ya maimaita kansa. Saboda gaggawata, na tsinci kaina a kurkuku, ina tafiya sannu-sannu a yanzu domin in rayu," cewar Buhari.

"Na taba shugabantar wannan kasar, wasunku sun sani a kwai lokacin da na taba zuwa cikin kakin soji, yadda na yi kuwa shi ne cafke kowa daga kan shugaban kasa har zuwa kasa. Shugaban kasa, mataimakinsa, gwamnoni da ministoci, banda shugaban kasa da mataimakinsa, sauran na turasu zuwa Kiri-Kiri, kuma na sanar da su cewa an kamasu da laifi, har sai idan sun kare kawunansu akan su masu gaskiya ne.

"Amma ai daga baya kun san me ya faru, mun kafa kotuna kusan guda shida bisa tsarin shiyya, wadanda suke ministoci da gwamnoni, muka su gabatar da hujjojinsu ta hanyar bayyana kadarorin da suka mallaka na rayuwarsu.

"Mutane biyu ne kawai daga cikinsu a iya sani na aka same su masu gaskiya, wadanda a yanzu sun rasu: Biliaminu Usman, wani karamin minista daga jihar Jigawa da kuma Adamu Chiroma, ministan kudi da babban bankin Nigeria.

"To amma fa nima ban tsira ba, daga bisani sai da aka cafke ni, aka garkame ni na tsawon shekaru ukku da kusan watanni hudu, inda na samun sa'a, ni ba wawa bane, ban saci kudin kowa ba, don haka ba a bata ni ba saboda basu samu wata hujja ta zargi a kaina ba.

"Daga bisani aka sake ni, wannan ne dalilin da ya sanya na tsunduma cikin siyasar farar hula. Kuma kunsan yadda komai ya faru, sau ukku ina takara ina faduwa, har sai a karo na hudu."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel