Zamfara: Za mu ba gwamnatin tarayya hadin kai – Shugaban kungiyar masu hakar ma’adinai

Zamfara: Za mu ba gwamnatin tarayya hadin kai – Shugaban kungiyar masu hakar ma’adinai

Kungiyar masu hakar ma’adinai ta Najeriya, tace za ta ba Gwamnatin Tarayya hadin kai, kan umurnin da tayi na tsayar da ayyukan hake-hake a Zamfara nan da sa’o’i 48.

Alhaji Kabir Kankara, babban shugaban kungiyar na kasa ya bayyana hakan nea ranar Talata, 10 ga watan Afrilu a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta tuna a baya cewa Gwamnatin Tarayya ta ba da umurni akan dakatar da dukkan ayyukan hake-hake a Zamfara nan da sa’o’i 48, a ranar 7 ga watan Afrilu.

Sufeto Janar na yan sanda, Muhammed Adamu, wanda ya ba da umurnin gwamnatin, yace umurnin tsayar da hake-haken na daga cikin matakan da aka dauka na magance lamarin ta’addanci a jihar.

Zamfara: Za mu ba gwamnatin tarayya hadin kai – Shugaban kungiyar masu hakar ma’adinai

Zamfara: Za mu ba gwamnatin tarayya hadin kai – Shugaban kungiyar masu hakar ma’adinai
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa umurnin ya biwo bayan wani bayanan sirri da ya hango alakar dake tsakanin ayyukan yan bindiga da kuma hake-haken ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa ta yiwa Atiku barazanar jefa shi a kurkuku

Kankara, har ila yau, ya bayyana cewa ba a ba da iyakan lokacin da za a dauka ana magance ayyukan yan bindigan ba daga wuraren da ake gudanar da hake-hake, ya kara da cewa yawancin mambobinsu sun kasance da manyan jari a harkan hake-hake a halin yanzu.

Ya ba gwamnati da hukumominta tabbacin cewa a shirye kungiyar take da ta basu hadin kai don tabbatar da zaman lafiya da kwazo a sashin ma’adanai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel