Reshe ya juye da mujiya: Sojoji sun bi sahun 'yan Boko Haram da su kayi yunkurin kai hari a Damataru

Reshe ya juye da mujiya: Sojoji sun bi sahun 'yan Boko Haram da su kayi yunkurin kai hari a Damataru

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta na bin sahun wata tawagar mayakan kungiyar Boko Haram da su kayi yunkurin kai hari a Damaturu, babban birnin jihar Yobe a ranar Talata.

A cikin sanarwar da ta fitar a daren Talata, Rundunar sojojin ta ce ta katse wa 'yan ta'addan hanzari ne sakamakon bayyanan sirri da ta samu game da harin da 'yan kungiyar suka shirya kaiwa a garin na Damaturu.

Sojojin sunyi ikirarin cewa sun kashe 'yan ta'adda da dama cikin sanarwar da mukadashin mataimakin jami'in hulda da jama'a na Sector 2 na Operation Lafiya Dole, Lt. Njoka Irabor ya fitar.

Harin Damaturu: Sojoji na bin sahun 'yan Boko Haram da ke tserewa - Hukumar Soji

Harin Damaturu: Sojoji na bin sahun 'yan Boko Haram da ke tserewa - Hukumar Soji
Source: UGC

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Wani bangare na sakon ya ce, "Bayan samun amintattun bayani a kan harin da 'yan Boko Haram ke shirin kaiwa Damaturu, Dakarun rundunar Sector 2 na Operation Lafiya Dole sun yiwa 'yan ta'addan kwantar bauna inda suka kashe da yawa cikinsu a yau Talata 9 ga watan Afrilu misalin karfe 5.15.

"Dakarun sojojin sunyi nasarar afkawa 'yan ta'addan a kusa da kauyen Maisandari da ke wajen garin Damaturu.

"Da dama cikin 'yan ta'addan sun gamu da ajalinsu yayin da wasu suka jikkata."

Sanarwar ta kuma ce sojojin sun kwato motocci masu dauke da bindiga guda biyu, AK 47 guda hudu, machine gun guda daya, bindiga mai harbo jiragen sama guda biyu, alburussai da sauransu.

Irabor kuma ya ce tuni sojojin sun fara bin sahun 'yan ta'addan da suka tsere tare da binciken kwa-kwaf a garin domin gano su.

Ya yi alkawarin bayar da karin bayani da zarar sojojin sun kammala aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel