An kama hanyar sakin layi a Majalisar Tarayya – Inji Sanata Ali Ndume

An kama hanyar sakin layi a Majalisar Tarayya – Inji Sanata Ali Ndume

A cikin ‘yan kwanakin nan da su ka gabata ne shugaban majalisar wakilai na tarayya watau Yakubu Dogara yayi jawabi a gaban sababbin ‘yan majalisun kasar inda ya tabo batun shugabancin majalisar.

A wajen wannan taro da aka shirya, Mohammed Ali Ndume wanda yana cikin masu harin kujerar shugaban majalisar dattawa, ya tofa albarkacin bakinsa a kan rigimar da ake faman yi a game da wanda za su rike majalisar.

Sanata Mohammed Ndume wanda ke shirin takara yake cewa a halin yanzu, an fara neman sakin layi daga kan turbar da aka kafa majalisar tarayya inda yake cewa wasu su na shirin maida majalisar kamar wani kayan gidan su.

KU KARANTA: Yakubu Dogara ya fadawa Sabon-shiga Majalisa wanda za su zaba

Mohammed Ali Ndume ya kara da cewa da zarar uwar jam’iyya ta bayyana yankin da za su fito da shugaba, abin da ya dace shi ne a kyale ‘yan majalisar kasar su duba, su fito da shugaban da su ke so ya jagoranci lamarinsu.

Sanatan yana ganin ‘yan majalisa su ne su ka san ciwon majalisa don haka kurum yake ganin a kyale wadanda su ke cikin daki su bayyana inda yake yi masu yoyo. Ndume ya sha alwashin ganin ya gaji Bukola Saraki a bana.

KU KARANTA: Wani Hadimin Jonathan yace Buhari babban makaryaci ne

Sanatan na Kudancin Borno ya kuma nuna rashin jin dadin sa game da yadda ake aiki a majalisa inda shugabannin majalisa ke da damar hana wani ‘dan majalisa da ya tashi domin yin bayani damar gabatar da jawabin sa.

Ali Ndume ya nemi a sake duban wannan tsari da idanun basira domin ganin an daina tauyewa wasu hakkin su. Shi dai Yakubu Dogara ya maidawa Sanatan martani da cewa idan ya samu mukami, zai gane wahalar aikin.

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyanawa ‘ya 'yan sa cewa zabin jam’iyyar shi ne dole a zabi Sanata Ahmad Lawan da kuma Honarabul Femi Gbajabiamilla a wannan karo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel