Fadar shugaban kasa ta yiwa Atiku barazanar jefa shi a kurkuku

Fadar shugaban kasa ta yiwa Atiku barazanar jefa shi a kurkuku

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman, Lauretta Onochie ta ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya godewa Allah da baya gidan kurkuku a yanzu.

A cewar hadiman shugaban kasar, ta gano hoton Atiku da ya sha kaye a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu da wasu rubutu masu ban mamaki a jikinsa.

Duk da cewa ba ta fadi takamamen abinda ta ga an rubuta a kan hoton na Atiku ba, ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya bawa kansa shawara kafin a tuhume shi da laifin cin amanar kasa.

Onuchie ta cigaba da cewa Atiku ya mayar da hankali a kan karar da ya shigar a kotu na kallubalantar nasarar Buhari a maimakon kitsa makirci.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

"Yanzu na dawo daga Abuja kuma na gano hoton Atiku tare da wasu rubutu masu ban mamaki.

"Wanda ya yi sa'ar cewa har yanzu ba a tsare shi ba, duk abinda ya ke shiryawa, kada ya manta muna da shugaban kasa.

"'Yan Najeriya za su bukaci a hukunta duk wanda ya ci amanar kasa. Ya kamata ya bawa kansa shawara.

"Idan ka sha kaye a zabe abinda ya kamata kayi shine ka taya wanda ya ci zaben murna ko kuma ka tafi kotu.

"Bayan jan kafa da ya yi tayi, Atiku ya tafi kotu yanzu. Zai fi dacewa ya mayar da hankali a kan shari'ar da akeyi a kotun a maimakon kokarin kitsa makirci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel