Ku manta da takarar shugabancin kasa a 2023, Okorocha ga kabilar Igbo

Ku manta da takarar shugabancin kasa a 2023, Okorocha ga kabilar Igbo

-Kuma ina fatan in samu takardata ta shedar lashe zabe daga INEC nan bada dadewa ba – Okorocha

-Gwamnan yayi kira ga a sake wani zabe tsakanin da takarar jam’iyar Action Alliance (AA), Uche Nwosu da Emeka Ihedioha

Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ya baiwa yan yankin Kudu maso Gabas ta Najeriya shawara da su manta da yunkurin tsayawa takara a shekarar 2023, yana mai cewa takarar kujerar ta ta’allaka ne zuwa ga Arewa da kuma Kudu maso Yamma.

Yace juya baya ga dan takarar All Progressives Congress (APC) wato Muhammadu Buhari izuwa ga dan takarar People’s Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar shine ya baiwa yankin matsala bisa ga aniyar tsayar takara nan da shekaru hudu masu zuwa.

Hukumar INEC

Hukumar INEC
Source: Getty Images

KARANTA: Rundunar 'yan sanda za ta bullo da sabbin dabarun samar da tsaro a Zamfara

Gwamnan wanda ya sanar da manema labarai yayin da yake bada bayani akan cigaban siyasa a jihar yace hakika abinda ya faru a zaben daya gabata a Kudu maso Gabas nakasu ne ga yankin igbo. Ya kara da cewa yana kyautata zaton cewa igbo ba zasu kara samun wakilci ba a tattaunawar jam’iyar APC ta kasa.

Har wa yau, yayi alkawarin sake dawo da martabar jam’iyar a jiharsa wadda ta kasance bata kawo dan majalisa ko guda ba a zaben da ya gabata.

Gwamnan ya soki hukumar zabe ta INEC saboda rashin yin abinda yakamata lokacin gudanar da zabe a jihar, yace abinda hakumar tayi sam bai dace ba kuma cin mutuncin demokradiyya ne ma.

Ya ce: “Kwamishinan zabe na jihar domin ya kawo cikas da kuma koma baya akan zabena wanda aka gabatar ba tare da magudi ba, kana shi kuma ya juya ilahirin wannan al’amari cewa zaben bai gudana cikin kyakkyawan yanayi ba.

“ Sama da jami’an jam’iyun siyasa saba’in, yan sanda da jami.an tsaro na farin kaya (DSS) na wannan wuri kuma sun karyata wannan zance cewa babu abinda ya faru a wannan waje, kuma ina fatan in samu takardata ta shedar lashe zabe daga INEC nan bada dadewa ba –ko kuma wa zasu baiwa?

Yana mai nuna rashin amincewarsa kan gabatar da dan takarar gwamna na jam’iyar PDP wato Emeka Ihedioha a matsayin wanda ya lashe zaben, a nashi cewar babu wanda ya lashe zaben karskashin bin kundin tsarin mulkin kasa.

Gwamnan yayi kira ga a sake wani zabe tsakanin da takarar jam’iyar Action Alliance (AA), Uche Nwosu da kuma takwaransa na PDP yana mai ikirarin cewa babu wani zabe da aka gudanar a idon shari’a.

“Idan da zaku duba abinda ya faru a Imo ta Arewa yayin zaben yan Majalisar dattijai da kuma Orlu, Orsu, Oru ta gabas, zaku fahimci cewa Kwamishinan zaben yazo yin wani gurbataccen aiki ne a wannan wuri.

“ A Orlu, inda aka bayyana cewa sakamakon zaben bai kamala ba, sai ga abin mamaki wani jami’in INEC ya fadi sunan wanda ya ci zabe.

“ A halin yanzu dai matsalolin dake tunkarar demokradiyar kasar kenan. Akwai yinkurin muzguna mana kuma ana amfani da INEC a matsayin makamin cin ma wannan buri don ganin cewa an jefa demokradiyya cikin matsala,” ya kara fadi.

Yayi ikirarin cewa murnar PDP zata koma ciki, a jihar saboda jam’iyar Action Alliance (AA) zata samu adalcin da take nema a karshe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel