A bayar da cikakken bayanin kasafin kudin majalisar dokokin kasar – Saraki yayi umurni

A bayar da cikakken bayanin kasafin kudin majalisar dokokin kasar – Saraki yayi umurni

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya baiwa magatakardan majalisar dokoki, Mohammed Sani-Omolori, umurnin bayyana cikakken bayanin kasafin kudin majalisar dokoki na 2019 don kaddamar dashi.

Wannan umurnin na kunshe ne a wani wasika da aka tura ma magatakardan mai dauke da kwanan wata 26 ga watan Maris, 2019.

Saraki ya sanar da cewa a bayyana cikakken bayanai kan kasafin kudin majalisar dokoki, a kuma gabatar dashi don kaddamar dashi a matsayin wani bangare na kasafin kudin kasa.

A bayar da cikakken bayanin kasafin kudin majalisar dokokin kasar – Saraki yayi umurni

A bayar da cikakken bayanin kasafin kudin majalisar dokokin kasar – Saraki yayi umurni
Source: Twitter

Wasikar na dauke da sa hannun shugaban ma’aikatun shugaban majalisa, Dr. Hakeem Ahmed.

KU KARANTA KUMA: Ina tafiyar hawaniya ne don na tsira - Buhari

Sashin wasikan ya zo kamar haka, “Shugaban majalisar dattawa ya bukace ni da inyi rokon cewa a tabbatar an bayyana kasafin kudin majalisar dokokin kasar tare da jerin kayayyaki don gabatar dashi tare da kasafin kudin kasa idan majalisar dattawa ta dawo bakin aiki a mako mai zuwa. Nagode”.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa akalla sanatoci 36 daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na goyon bayan Ali Ndume, sanata mai wakiltan jama'ar Borno ta kudu a majalisar dattawa wanda ke neman kujeran shugaban majalisar dattawa, wani zababben sanata da aka sakaye sunansa ya laburta.

Zababben sanatan wanda dan Arewa ne ya bayyana hakan ne ranar Talata, 10 ga watan Afrilu yayinda yake magana da wasu manema labarai a wajen taron ilmantar da sabbin yan majalisa dake gudana a Transcorp Hilton hotel Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel