Babbar magana: Shugaba Buhari makaryaci ne, ina da dalilan fadin hakan - Omokri

Babbar magana: Shugaba Buhari makaryaci ne, ina da dalilan fadin hakan - Omokri

- Omokri, wanda mamba ne a ofishin yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar PDP, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin makaryaci

- Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ana shigo da buhunan shinkafa 20m zuwa kasar ta barauniyar hanya duk da dokar da Buhari ya sanya

- Da ya ke martani kan hakan, tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana tsare tsaren gwamnatin Buhari a matsayin na bogi

Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya sake caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Omokri, wanda mamba ne a ofishin yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar PDP, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin makaryaci.

Ya bayyana hakan a lokacin da ya ke mayar da martani kan wani ikirari da gwamnatin tarayya ta yi na cewar Nigeria a yanzu ta bunkasa ta fannin samar da shinkafa.

Rahotanni dai sun bayyana cewa har yanzu ana shigowa da buhunan shinkafa miliyan ashirin zuwa kasar ta barauniyar hanya duk da dokar haramta shigo da shinkafar da Buhari ya sanya.

KARANTA WANNAN: Mu leka kotu: Ina da shekaru 11 Baba 90 ya fara lalata da ni - Yar shekaru 13

Omokri

Omokri
Source: Instagram

Da ya ke martani kan hakan, tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana tsare tsaren gwamnatin Buhari a matsayin na bogi.

A shafinsa na Twitter, Omokri ya wallafa cewa: "Duk yadda karya ta yi nisan zango, karshe sai gaskiya ta riske ta ta murkushe ta. A lokacin da Buhari ya ce gwamnatinsa ta sanya 'yan Nigeria na iya samar da isassar shinkafa, ni kuma na fito na ce karya ne.

"Yanzu dai ai gashi gaskiya ta bayyana, ba wai daga gareni ko 'yan siyasa ba, amma daga manoman shinkafar da kansu."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel