Muhimman abubuwan cigaba da Buhari ya tattauna da Yariman Abu Dhabi

Muhimman abubuwan cigaba da Buhari ya tattauna da Yariman Abu Dhabi

A ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Dubai, sunyi wata muhimmiyar tattaunawa da Yariman Abu Dhabi, domin kawo cigaba ga kasashen guda biyu

A jiya Talala ne 9 ga watan Afrilu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Yarima mai jiran gado na hadaddiyar daular larabawa, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, suka kara tabbatar da bukatar yin aiki tare domin kawo cigaba da kuma karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen guda biyu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Yariman Abu Dhabi sun hadu a birnin Abu Dhabi, in da su ka tattauna akan hanyoyin da za su bi domin kara dankon zumunta tsakanin Najeriya da hadaddiyar daular larabawa (UAE).

Muhimman abubuwan cigaba da Buhari ya tattauna da Yariman Abu Dhabi

Muhimman abubuwan cigaba da Buhari ya tattauna da Yariman Abu Dhabi
Source: UGC

Bayan tabbatar da cewa kasashen biyu suna jin dadin cinikayya da junansu, shugabannin kasashen biyu sunyi alkawarin cigaba da kasuwanci.

Bayan haka kuma shugabannin sun tattauna akan hanyar da za su bi domin kawo cigaba a bangaren ilimi, kiwon lafiya, noma, da dai sauransu.

Yayinda kasashen biyu suke da yawan matasa, shugaba Buhari da Yariman Abu Dhabi sunyi musayar ra'ayoyi akan yadda zasu kawo cigaba ga al'umma masu tasowa.

KU KARANTA: Bankin musulunci ya bawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 532

Bugu da kari kuma, shugabannin biyu sun tattauna game da hanyoyin bunkasa tattalin arziki, ta fannin man fetur, da kuma matsalolin tsaron da ke addabar nahiyar Afirka da kuma kuma yankin gabas ta tsakiya.

A karshe Yariman ya taya shugaba Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu, sannan kuma ya yi masa addu'ar nasara a sabuwar gwamnatin da zai kafa karo na biyu.

Har ila yau Yariman ya bayyana kudurin kasar tasu na zuba hannun jari a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel