Zaben 2019: APC da sauran jam’iyyu sun yi cinikin kuri’u - Auwalu

Zaben 2019: APC da sauran jam’iyyu sun yi cinikin kuri’u - Auwalu

Dan siyasa kuma ma’ajin kudi na jam’iyyar Youth Party (YP) na kasa, Aminu Auwalu, yayi bayanin darasin da ya koya a lokacin da yake neman takarar kujerar mamba a majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Tarauni, jihar Kano a zaben kwanan nan da aka kammala na 2019.

A wata hira da yayi da Legit.ng, Auwalu, wanda ya nemi takara karkashin jam’iyyar YP yayi ikirarin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran manyan jam’iyyun siyasar Najeriya sun yi cinikin kuri’u a zaben.

A cewarsa, ana ta ba mutane kyaututtuka da kudade don su siyar da yancinsu ta hanyar zabar wanin muradinsu a yayin zabe.

Zaben 2019: APC da sauran jam’iyyu sun yi cinikin kuri’u - Auwalu

Zaben 2019: APC da sauran jam’iyyu sun yi cinikin kuri’u - Auwalu
Source: Facebook

Ya bayyana cewa nasara irin wadannan mutane baya bisa ka’ida domin siyan kuri’u ya kasance ne sanadiyar halin talauci da yan Najeriya da dama ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Ina tafiyar hawaniya ne don na tsira - Buhari

Ya kuma bayyana cewa kamata yayi ace siyasa ya zamo macecin mutane amma abun bakin ciki, ya zamo ba komai ba face hanyar jefa mutane cikin kangi.

Da yake ci gaba da bayani akan sakamakon zaben, Auwalu ya kuma yi ikirarin cewa babu wani sakamako da aka saki a Kano amma aka kaddamar da dan takarar APC, Hafizu Kawu a matsayin mai nasara a mazabar Tarauni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel