Da duminsa: Masu garkuwa sun sako shugaban hukumar kashe gobara ta Legas

Da duminsa: Masu garkuwa sun sako shugaban hukumar kashe gobara ta Legas

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Legas ta tabbatar da cewa an sako shugaban hukumar kiyaye gobara ta jihar, Rasaki Musibau da masu sace mutane su kayi garkuwa da shi kwanaki uku da suka gabata.

A cewar Kakakin 'yan sandan jihar Legas, DSP Bala Elkana, an sako Musibau da sauran mutane shida da aka sace su misalin karfe 11.45 na daren Talata 9 ga watan Afrilu.

Elkana ya tabbatar da cewa an sace su ne a ranar 6 ga watan Afrilu a unguwar Ketu-Ereyun na jihar Legas amma a halin yanzu suna tare da iyalansu yayin da 'yan sanda ke cigaba da bincike dajin ikorodu domin bin sahun masu garkuwa da mutanen.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Da duminsa: Masu garkuwa sun sako shugaban hukumar kashe gobara ta Legas

Da duminsa: Masu garkuwa sun sako shugaban hukumar kashe gobara ta Legas
Source: UGC

"Dukkan wadanda a kayi garkuwa da su sun koma wurin iyalansu.

"Tawagar 'yan sanda tana nan tana cigaba da bincike a daji domin bin sahun masu garkuwa da mutanen.

"An tsaurara matakan tsaro a duk sassan jihar domin kare afkuwar irin wannan a gaba," a cewa Elkana yayin da ya ke yabawa al'ummar jihar bisa gundunmawar da suke bawa rundunar.

Ya kuma mika godiya ta musamman ga mazauna unguwar da suka taimakawa 'yan sanda da bayanai masu muhimmanci da ya taimaka wurin ceto wadanda akayi garkuwa da su.

"Tare da ku za mu tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a jihar Legas da sauran jihohin Najeriya," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel