Ina tafiyar hawaniya ne don na tsira - Buhari

Ina tafiyar hawaniya ne don na tsira - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai damu da wadanda ke kiransa da suna ‘Baba go slow’ wato mai tafiyar hawainiya ba

- Buhari yace baya so ya sake tafka irin kuskuren da yayi a lokacin da yake a matsayin shugaban kasa a mulkin soja lokacin da yake ta gaggawa

- Yace yana akan ne domin ya tsiratar da kansa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu ya bayyana cewa bai damu da wadanda ke kiransa da suna ‘Baba go slow’ wato mai tafiyar hawainiya ba.

A cewarsa, baya so ya sake tafka irin kuskuren da yayi a lokacin da yake a matsayin shugaban kasa a mulkin soja lokacin da yake ta gaggawa.

Yanzu, yace yana tafiyar hawainiya ne domin ya tsira.

Shugaban kasar na amsa wasu tambayoyi ne a lokacin wani taron yan Najeriya a Dubai.

Ina tafiyar hawaniya ne don na tsira - Buhari

Ina tafiyar hawaniya ne don na tsira - Buhari
Source: Twitter

A cewarsa, daya daga cikin dalilan da suka sa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda ya ki hadiye abunda shi (Buhari) yayi masa bayani akan rikicin makiyaya da manoma a jihar.

Buhari ya bayyana cewa yayi na Ortom bayanin cewa matsalar makiyaya da manoma a Najeriya ya girme masa (Buhari) balle shi (Ortom).

KU KARANTA KUMA: Idan kaji ana ki gudu, sa gudu ne bai zo ba: Kalli yadda Sojoji suka kama shugaban masu garkuwa

Shugaban kasar ya bayyana ma kungiyar cewa gwamnatinsa ta dauki mataki kan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba wanda ke gudana a jihar Zamfara wanda ke da nasaba da fashi da hare-haren da ake kai wa jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel