Rundunar 'yan sanda za ta bullo da sabbin dabarun samar da tsaro a Zamfara

Rundunar 'yan sanda za ta bullo da sabbin dabarun samar da tsaro a Zamfara

Sufeta Janar na 'yan sanda na kasa, Mr Mohammed Adamu ya sanar da cewa rundunar za ta bullo da sabbin dabaru domin kawo karshen kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar Zamfara.

Adamu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a garin Gusau yayin da ya kai ziyarar ganin ido a kan halin da ake ciki.

Ya ce dakatar da hakar ma'adinai a jihar da gwamnatin tarayya tayi yana daya daga cikin sabbin dabarun na magance kallubalen tsaron.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta kori manyan jami'an ta 9 saboda saba dokar aiki

Rundunar 'yan sanda za ta bullo da sabbin dabarun samar da tsaro a Zamfara

Rundunar 'yan sanda za ta bullo da sabbin dabarun samar da tsaro a Zamfara
Source: UGC

"Mun fahimci cewa akwai alaka tsakanin bata gari da wadanda suka hakar ma'adinai kuma mun gano wasu mutanen da suka hada kai da masu aikata laifukan wadanda za mu kama nan ba da dade wa ba.

"Mun dau alwashin yanke duk wata hulda da masu aikata laifuka su ke da shi da jihar sannan mu fattataki 'yan bindiga daga dukka sassan jihar," inji shi.

A jawabinsa, Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya yabawa Gwamnatin Tarayya bisa sabon yunkurin da tayi na magance matsalar tsaro a jihar.

Yari, wanda ya samu wakilicin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abdullahi Shinkafi ya jadada niyyar gwamnatin jihar na hadin gwiwa da sauran hukumomi domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Ya yi kira ga shugaban na 'yan sanda ya karo wasu jami'ai zuwa jihar domin magance kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar.

Ya ce gwamnatin jihar ta dauki matasa 8,500 daga masarautu 17 na jihar domin tallafawa gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel