Shin zababben Gwamnan Adamawa Fintiri, ya shirya kuwa?

Shin zababben Gwamnan Adamawa Fintiri, ya shirya kuwa?

- Kafin Fintiri ya samu gudanar da gwamnatinsa cikin tsanaki ya zama wajibi a gareshi yayi shagube tsakanin dokoki da kuma siyasa.

- Ranar 29 ga watan Mayu, Fintiri zai dawo a matsayin Gwamnan Adamawa a wannan lokaci da ake da bukatar ayyuka da dama da kuma kyautata zato a kansa.

Zababben Gwamnan Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya zamo fitacce ne kuma jigo a siyasa cikin wata uku kacal a shekarar 2014.

Alal hakika yan makonni kalilan gabanin zamansa Gwamna mai rikon kwarya a shekarar 2014, idan ka ce dashi zai zamo dan takarar Gwamna karkashin jam’iyar PDP a shekarar 2019 zai ce wasa kakeyi.

Cikin kankanin lokaci bayan ya karba ragamar jagoranci ya sauya yanayin Adamawa musamman fannin gine-gine da kuma walwalar ma’aikata. Kai harma wadanda basu goyon bayansa sun shaida hakan.

Ahmadu Fintiri

Ahmadu Fintiri
Source: UGC

Ranar 29 ga watan Mayu, Fintiri zai dawo a matsayin Gwamnan Adamawa a wannan lokaci da ake da bukatar ayyuka da dama da kuma kyautata zato a kansa. Yanda zai magance wadannan matsaloli zai gyara masa siyasarsa da karin farin jini wurin jama’a ko kuma akasin haka.

KU KARANTA:Buhari ya taikaita tafiyar sa, ya dawo daga Dubai

Kafin Fintiri ya samu gudanar da gwamnatinsa cikin tsanaki ya zama wajibi a gareshi yayi shagube tsakanin dokoki da kuma siyasa. Babu Gwamnan da ya samu nasarar kawo cigaba a Adamawa ba tare da ya yi azancin ajiye siyasa a gefe ba yayin da ya shiga ofis.

Harkokin kananan hukumomi, ilimi, walwalar ma’aikata da kuma cigaban matasa na daga cikin sassan da Fintiri ke da bukatar mayar da hankali a kai sosai. Gazawar Gwamna Bindow mai murabus ta wannan fannin ya haifar masa da matsala babba a wajen neman a sake zabensa a karo na biyu.

Akwai bukatar Fintitri ya farfado da cibiyar koyar da sana’a a wurare daban daban a fadin jihar. A sake bunkasasu da kayan aiki don koyar da sana’a saboda arziki ya wadata.

Har wa yau wadannan cibiyoyi yakamata a kara ingantasu ta hanyar shigo da harkokin noma a cikinsu. Hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen kara habbaka tattalin arziki da kuma cigaba.

Yin hakan zai karfafa mazauna karkara tare da bada ta su gudumawar wajen bunkasa tattalin arziki.

Fintiri ya lashe zabe ne saboda hadin gwiwa da wasu dabaru dai na siyasa. Don haka akwai bukatar ya bayyana karara yanda mutane zasu fahimci salon siyasarsa a fili. Hakan ne yasa akwai babban kalubale a gabansa don ya tabbatar cewa ya yi abinda ya dace.

A shekarar 2014 jiga jigai a jihar sun fada cewa yana nuna bambanci ga mutane kalilan kuma zancen nasu yayi tasiri. Sai dai kash, hakan bai samu karbuwa ba a 2019.

Akwai bukatar Fintiri ya mance da baya domin ya hari gaba ya kuma samu ya fadada tsarin aikinsa. Ya kasance yayi aiki da hausa-fulani, kautal pulaku, wanda suke rike da kashi tamanin da biyar cikin dari na arzikin jihar.

Hakan zai taimaka masa wajen samun karbuwa ga dukkanin al’umomin jihar. Duk dai cewa ba zai iya wadatar da su ba gaba daya, amma dai zai iya ya riki kowa na shi domin a tafi tare.

Zuwa 29 ga watan Mayu, Fintiri zai fuskanci sa ido da kuma suka daga bakin manyan yan siyasa na Adamawa da kuma dai-daikun mutane. Shin ya shirya

Daga Zayyad I. Muhammad Jimeta

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU DANNA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel