Dakarun sojin Najeriya sun samu galaba kan Yan Boko Haram da sukayi kokarin shiga Damaturu (Hotuna)

Dakarun sojin Najeriya sun samu galaba kan Yan Boko Haram da sukayi kokarin shiga Damaturu (Hotuna)

Jami'an rundunar Operation Lafiya Dole sun samu gagarumin nasara kan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram da suka kai hari birnin Damaturu da yammacin Talata, 9 ga watan Afrilu, 2019.

Mataimakin kakakin hukumar sojin Operation Lafiya dole, Njoka Irabor, ya bayyana hakan ne a wani jawabin da ya saki da safiyar Laraba inda yace:

"Bisa ga labarin da muka samu cewa yan Boko Haram sun yi kokarin kai hari Damaturu, jami'an sojin Sector 2, Operation LAFIYA DOLE, sun samu nasara dira kan yan ta'addan kuma aka samu nasarar hallaka yan Boko Haram da dama misalin karfe 5:15 na yammacin Talata, 9 ga watan Afrilu 2019."

"Jaruman sojin sun ragargaji yan ta'addan kuma da Maisandari, dake kusa da birnin Damaturu. Wutan sojin kasa da luran jami'an sojin sama ya galabi yan ta'addan."

Sakamakon haka yan ta'addan da dama sun gamu da ajalinsu kuma wasu sun samu raunuka inda aka kwato makamai kamar haka:

a. Motocin Bindiga 2

b. Bindigogin baro jirage 2

c. 1 x 60 Millimetre Mortar .

d. Bindigar AK47 hudu

e. Bindiga mai carbi

f. Harsasai 1,245

Kana sojin sun bazama neman yan ta'addan da suka gdud kuma ana cigaba da neman sauran."

Source: Legit

Tags:
Online view pixel