Kungiyar dattawan Arewa zata gudanar da taron gaggawa don tattauna matsalar tsaro

Kungiyar dattawan Arewa zata gudanar da taron gaggawa don tattauna matsalar tsaro

Duba da halin da yankin Arewacin Najeriya ta tsinci kanta a ciki na ayyukan barayi masu garkuwa da mutane da kuma matsalar hare haren yan bindiga, kungiyar tuntuba ta Arewacin Najeriya, watau ACF ta shirya taron gaggawa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar amintattu ta wannan kungiya zata gana ne a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a garin Kaduna, inda ake sa ran zasu tattauna akan matsalolin kashe kashe da na satar mutane don neman kudin fansa daya addabi yankin Arewa.

KU KARANTA: Babu gagararre sai bararre: Yadda mayakan Sojan sama suka halaka yan bindiga

Kungiyar dattawan Arewa zata gudanar da taron gaggawa don tattauna matsalar tsaro

Kungiyar dattawan Arewa
Source: Facebook

Kaakakin kungiyar, Alhaji Mohammed Biu ya tabbatar da shirya wannan taron gaggawa, inda yace kungiyar tuntuba ta Arewa ta damu matuka da duba da sabon salon matsalar tsaro dake nema ya cinye Arewacin Najeriya.

Sai dai wannan taro na ACF yazo ne a daidai lokacin da Ministan tsaro, Mansur Dan Ali ya zargi wasu sarakan gargajiya da hannu a cikin matsalar tsaron da ake fuskanta a Arewa, amma Muhammed Biu ya ki cewa komai game da wannan zargi.

“Kungiyar tuntuba ta Arewa ta damu matuka game da rahotannin da take samu na yadda wasu miyagu ke garkuwa da mutanen da basu ji ba, basu gani ba akan babbar hanyar Kaudna zuwa Abuja, da kuma hare haren yan bindiga a kauyukan Zamfara, Sokoto, Katsina da Kaduna, wannan zalunci ne.” Inji Biu.

A wani labarin kuma rundunar Sojan sama ta sanar da cewa mayakanta sun samu nasarar halaka yan bindiga guda dai dai har guda ashirin da biyar a jahar Zamfara, yayin da ta jikkata wasu da dama a wasu hare hare data kaddamar musu da jiragen yakinta.

Kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka, inda yace Sojojin sun kai wannan hari ne a karkashin aikin Operation Diran Mikiya bayan samun bayanan sirri game taruwar yan bindiga a sansaninsu dake Ajia.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel