Shugabancin majalisa: Sanatocin APC 36 ke goyon bayan Ali Ndume

Shugabancin majalisa: Sanatocin APC 36 ke goyon bayan Ali Ndume

- Zawarcin kujerar majalisar dattawa na cigaba da zafi

- Zuwa yanzu, sanatoci 3 ke kan gaba wajen neman kujerar

- Sanata Ali Ndume ya lashi takobin cewa ba zai janye ba

Akalla sanatoci 36 daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na goyon bayan Ali Ndume, sanata mai wakiltan jama'ar Borno ta kudu a majalisar dattawa wanda ke neman kujeran shugaban majalisar dattawa, wani zababben sanata da aka sakaye sunansa ya laburta.

Zababben sanatan wanda dan Arewa ne ya bayyana hakan ne ranar Talata, 10 ga watan Afrilu yayinda yake magana da wasu manema labarai a wajen taron ilmantar da sabbin yan majalisa dake gudana a Transcorp Hilton hotel Abuja.

Duk da cewa jam'iyyar APC ta marawa Sanata Ahmed Lawan baya, Ndume ya lashi takobin cigaba da takararsa.

KU KARANTA: Gabanin tasowa daga kasar UAE, Buhari ya gana da Yariman Abu Dhabi (Hotuna)

Bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ranar Litinin, Ndume ya bayyanawa manema labarai cewa babu gudu ba ja da baya.

Zababben sanatan ya ce wasu sanatoci na fushi saboda an rigaya da raba kwamitoci masu kyau ga masu goyon bayan Lawan.

Yace: "Akwai kimanin zababbun sanatoci 36 da ke goyon bayan Ndume kuma hakan ya faru ne saboda yadda suke gudanar da shirin zaben kujerar shugaban majalisa."

"Ta yaya Lawan zai yi tunanin cewa sanatocin APC sun yi masa sadakar zababbun sanatoci a zaben kujerar. Sun rabawa kawunansu kwamitoci babu mu. Ba'a abu haka."

Ya ce wadanda ke goyon bayan Ndume na fushi kan yadda Adam Oshiomole , shugaban APC ke kama karya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel