Majalisar dattawa ta yi amanna da nadin mukaman Buhari a hukumar NBS

Majalisar dattawa ta yi amanna da nadin mukaman Buhari a hukumar NBS

Da sanadin jaridar The Punch mun samu cewa, a ranar Alhamis majalisar dattawan Najeriya, ta yi amanna da nadin mukaman shugaban kasa Muhammadu Buhari a hukumar kididdiga ta kasa NBS, National Bureau of Statistics.

Majalisar dattawa kamar yadda rahotanni suka bayyana, ta yi amanna da kudirin shugaban kasa Buhari, biyo bayan rahoto na sakamakon bincike da kwamitin ta akan tsare-tsaren kasa da kuma tattalin arziki ya gabatar.

Majalisar dattawa ta yi amanna da nadin mukaman Buhari a hukumar NBS

Majalisar dattawa ta yi amanna da nadin mukaman Buhari a hukumar NBS
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar ta amince da Kabiru Nakaura, a matsayin shugaban hukumar NBS mai wakilcin reshen Arewa maso Yamma. Shugaban kasa Buhari ya mika sunayen wadanda za su jagoranci hukumar NBS tun a watan Nuwamba na 2018.

Sauran shugabannin hukumar da majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mukaman su sun hadar da; Akinola Bashir (Kudu maso Yamma), Moses Momoh (Kudu maso Kudu), Wallijoh Ahijoh (Arewa ta Tsakiya), Adam Modu (Arewa maso Gabas), da kuma Nwafor Chukwudi (Kudu maso Gabas).

KARANTA KUMA: Buhari ya umurci shugabannin tsaro a kan kada su ragawa masu ta'addanci a Najeriya

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya taya sabbin shugabannin hukumar murna tare da yi masu fatan alheri gami da gargadi a kan jajircewa wajen yiwa kasar su ta Najeriya hidima.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel