Buhari ya umurci shugabannin tsaro a kan kada su ragawa masu ta'addanci a Najeriya

Buhari ya umurci shugabannin tsaro a kan kada su ragawa masu ta'addanci a Najeriya

A yayin da ta'addanci ya kai mataki na intaha a jihar Zamfara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya harzuka inda a ranar Alhamis ya gindayawa shugabannin tsaro na kasa wani muhimmin umurni na ba bu sani ba bu sabo.

Shugabannin tsaro na Najeriya a fadar shugaban kasa

Shugabannin tsaro na Najeriya a fadar shugaban kasa
Source: Facebook

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya umarci dukkanin hukumomin tsaro na kasa a kan kada su rangwantawa masu haifar da ta'addanci a jihar Zamfara da kuma kewayen ta gami da sauran sassa na kasar nan.

KARANTA KUMA: Za a buga wasan kwallon kafa domin yiwa Gwamna Ambode bankwana na barin gado

Shugaban ma'aikatan tsaro na kasa, Janar Gabriel Olanisakin, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin wata hira da manema labarai a fadar shugaban kasa ta Villa da ke garin Abuja bayan ganawar su da ta tsawon awanni biyu da shugaban kasa Buhari.

Kazalika yayin shaidawa shugaban kasa Buhari yanayi na matakan tsaro da hukumar 'yan sanda ta dauka, mukaddashin sufeton 'yan sanda na kasa, Muhammadu Adamu ya bayyana cewa, a halin yanzu hanyar Abuja zuwa Kaduna ta tsarkaka daga masu ta'adar garkuwa da mutane.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel