Za a buga wasan kwallon kafa domin yiwa Gwamna Ambode bankwana na barin gado

Za a buga wasan kwallon kafa domin yiwa Gwamna Ambode bankwana na barin gado

Za ku ji cewa an fara shirye-shiryen yiwa gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, bankwana na barin gado, inda wasu fitattun 'yan kwallon kafa na duniya za su taka leda a ranar 18 ga watan Mayu domin karamci a gare sa.

Gwamna Ambode tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa

Gwamna Ambode tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa
Source: Twitter

Shugaban kwamitin hada kwallon ta bankwana, Wahidi Akanni, tsohon na wasan Najeriya, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba. Ya ce wasu fitattun 'yan kwallon kafa na duniya za ataka leda domin yiwa gwamna Ambode bankwana na barin gado.

Bayan shafe tsawon shekaru hudu na wa'adi daya kacal a bisa karagar mulki ta gwamnatin jihar Legas, za a taka leda domin yiwa gwamna Ambode bankwana kwanaki 11 gabanin ya sauka daga kujerar sa a ranar 29 ga watan Mayu.

A yayin da za a buga wasan kwallon kafar a filin wasanni na Onikan da ke jihar Legas, mashahuran 'yan kwallon kafar da za su taka leda sun hadar da Didier Drogba na kasar Ivory Coast, George Weah da a halin yanzu ya kasance shugaban kasar Liberia.

KARANTA KUMA: Ababe 10 da hukumar JAMB ta hana shiga dakin jarrabawa da su

Sauran manyan 'yan kwallon kafa na nahiyyar Afirka da za su motsa yayin yiwa gwamna Ambode bankwana sun hadar da Samuel Eto'o na kasar Kamaru da kuma Michael Essien na kasar Ghana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel