Ababe 10 da hukumar JAMB ta hana shiga dakin jarrabawa da su

Ababe 10 da hukumar JAMB ta hana shiga dakin jarrabawa da su

A yayin da a yau Alhamis, 11, ga watan Afrilun 2019, aka fara gudanar da jarrabawar neman shiga jami'a da hukumar JAMB ke shiryawa a fadin kasar nan, an haramtawa dalibai shiga da wasu ababe dakin jarrabawa.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, za a gudanar da jarrabawar cikin jihohi 36 da ke fadin kasar nan da kuma birnin tarayya. Ana sa ran za a shafe tsawon mako guda gabanin kammala jarrabawar.

Kakakin hukumar JAMB cikin wata hirar sa da mamena a daren Larabar da ta gabata, ya ce akwai wasu ababe da hukumar ta haramtawa dalibai shiga da su dakin jarrabawa domin tabbatar da tsari da kuma aminci na hukumar.

KARANTA KUMA: Ba mu da nufin daukan masu ribatar shirin N-Power a matsayin ma'aikatan gwamnati - Gwamnatin tarayya

Kimanin dalibai miliyan 1.99 masu neman shiga jami'o'i za su zana jarrabawar a bana cikin fadin kasar nan. Ana horar da su akan bibiyar tsari da kiyaye duk wata doka da kuma sharadi da hukumar ta gindaya.

Jaridar Legit.ng ta kawo jerin ababe da hukumar ta haramtawa dalibai shiga da su dakin jarrabawa kamar haka:

1. Agogo

2. Fensir/Biro

3. Na'urar lissafi (Kwakuleta)

4. Wayoyin Salula

5. Na'urar daukan hoto (Kamera)

6. Na'urorin sauraro da watsa sauti

7. Katin Banki (ATM)

8. Abin goge rubutu (Kilina)

9. Littafin da dukkanin dangin kayan karatu da rubutu

10. Yari da zobe masu fasahar zamani

11. Na'urorin ajiya na USB, CD da Hard disks

12. Tabarau mai kunshe da fasahar zamani

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel