Murnar samun nasara: Abba gida-gida ya yiwa Gwamna Ganduje raddi

Murnar samun nasara: Abba gida-gida ya yiwa Gwamna Ganduje raddi

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana mamakin sa dangane yadda hirar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ta kasance da wata kafar wata labarai kan karashen zaben jihar da ya gudana.

Abba Yusuf wanda ya shahara da inkiyar Abba gida-gida, ya bayyana mamakin sa, sakamakon yadda gwamna Ganduje ya ke ci gaba da murnar samun nasarar cin zabe duk da miyagun ababe na rashin gaskiya, murdiya, da kuma magudi da suka mamaye shi.

Abba Kabir Yusuf

Abba Kabir Yusuf
Source: UGC

Cikin wata sanarwa da sanadin kakakin sa, Sanusi Dawakin Tofa, Abba gida-gida ya ce gwamna Ganduje ya ribaci miyagun 'yan ta'ada wajen cin karen su ba bu babbaka domin rinjayar da nasara tare da danne hakkin al'ummar jihar Kano.

Dan takarar na jam'iyyar PDP ya yi babatun yadda gwamna Ganduje ya take sani da kuma gaskiya wajen ci gaba da bugun gaba da bayyana farin cikin samun nasara duk irin ababe na rashin kunya da rashin tsoron Mahallacin sa da ya aikata yayin zaben Kano.

KARANTA KUMA: Ba mu da nufin daukan masu ribatar shirin N-Power a matsayin ma'aikatan gwamnati - Gwamnatin tarayya

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ganduje a makon da ya gabata ya yi ikirarin cewa, jam'iyyar PDP tare da hadin gwiwar kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, Muhammad Wakil, ta tafka ababe na murdiya da magudi yayin zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel