Ba mu da nufin daukan masu ribatar shirin N-Power a matsayin ma'aikatan gwamnati - Gwamnatin tarayya

Ba mu da nufin daukan masu ribatar shirin N-Power a matsayin ma'aikatan gwamnati - Gwamnatin tarayya

Da sanadin kafar watsa labarai ta jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnatin tarayya ta yi watsi da rade-radin da ke yaduwa kan cewa za ta sanya masu ribatar shirin N-Power cikin sahun ma'aikatan gwamnati.

Babban hadimi na musamman ga shugaban kasa Buhari akan samar da ayyukan yi da bai wa Matasa tallafi, Mista Afolabi Imoukhuede, shi ne ya yi watsi da jita-jitar yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Laraba cikin garin Abuja.

Ba mu da nufin daukan masu ribatar shirin N-Power a matsayin ma'aikatan gwamnati - Gwamnatin tarayya

Ba mu da nufin daukan masu ribatar shirin N-Power a matsayin ma'aikatan gwamnati - Gwamnatin tarayya
Source: UGC

Mista Imoukhuede ya ce a iyaka sanin sa gwamnatin tarayya ba ta da nufin aiwatar da wannan lamari kuma ya na yakinin cewa ba bu inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba furta kalami makamancin wannan.

Hadimin na shugaban kasa ya ce, gwamnatin tarayya ta bai wa masu ribatar shirin N-Power damar ci gaba da ayyukan su duk da karkewar wa'adin su kuma za ta ci gaba da biyan su alawus kamar yadda ta saba.

A yayin da a kafofi da dandalan sada zumunta ake ci gaba da rade-radin gwamnatin tarayya za ta sanya masu ribatar shirin N-Power cikin sahun ma'aikatan gwamnati, Mista Imoukhuede ya ce ba bu wannan batu illa iyaka kudirin gwamnatin na inganta shirin domin fadada yalwar sa.

KARANTA KUMA: Sarkin Musulmi ya nemi hukumar 'yan sanda ta kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Sai dai ya ce akwai yiwuwar gwamnati za ta sauya shawara inda a halin yanzu masu kula da shirin N-Power ke ci gaba da tuntubar wasu gwamnoni a kan sanya masu ribatar shirin cikin sahun ma'aikatan gwamnatin su.

Hadimin na shugaban kasa Buhari ya yi amanna dangane da yadda wasu daga cikin masu hidimar shirin N-Power ke taka muhimmiyar rawa tare da bayar da gudunmuwa mai girman gaske musamman a bangaren karantarwa da bayar da ilimi a makarantu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel